Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so

Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so

- Yankin Gilgil a kasar Kenya ya shiga rudani bayan wasu maza masu aure sun kashe kansu har lahira

- Mazan biyu sun sassari kansu da adda ne bayan sun gano mace daya suke nema na wajen shekaru biyu

- Wannan ya faru ne bayan kwanaki kadan da wani magidanci ya kusa halaka mahaucin da ke lalata da matar shi tare da bata nama kyauta

Wasu masu sana'ar shanu sun yi fadan da ya kai ga har suka halaka junansu, duk kuwa a kan mace.

Dukkan mazan biyu kuwa masu aure ne kuma an gano sun yi fadan ne a Ojorai da ke Gilgil a Ghana.

Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so

Magidanta sun kashe kansu da adduna akan budurwar da suka shafe shekara 2 suna so
Source: Facebook

Masu kallo sun sha matukar mamakin yadda suka hari juna da adduna. Daya an datse shi ne a wuya da addar inda ya fadi matacce a take. Dayan kuma ya fadi ya mutu ne a wani daji da ke da kusanci da cibiyar kiwon lafiyan garin.

A yayin tattaunawa a kan aukuwar lamarin, Kwamishinan Gilgil, Ndambuki Mutheki ya ce 'yan sanda na bincikar lamarin. Ya kara da cewa ana tuhumar matar da ake zargin sun yi fada a kai.

Wani shaida mai suna Abel Kiprokon ya bayyana cewa mazan biyu na neman matar mai yara uku ne na kusan shekaru biyu ba tare da sun sani ba.

Dukkan mazan suna da aure kuma basu san juna ba har safiyar Laraba yayin da daya ya tarar da dayan yana kalaci.

KU KARANTA: Matar da ta kamu da Coronavirus ta arce daga wajen magani ta sha alwashin gogawa duk wanda yayi kokarin kama ta

"Sun hari juna da adda," Kiprokon yace.

Wannan na zuwa ne bayan rahoton wani mahaucin da ya tsallake mutuwa bayan ya ja wata mace da nama don lalata.

Sa'ar shi ta kare ne bayan ya fada tarkon da mijinta ya saka mishi bayan ya gano yana lalata da matarshi.

Bayan mijin ya samu rahoto daga makwabtan shi cewa mahaucin wanda aka fi sani da Akwai Teta, yana kwance da matarshi, sai ya dawo gida.

Mijin ya tarar da Teta tare da matar shi wanda hakan yasa ya bi shi da bulala.

Mahaucin ya gudu bayan da mijin ya shiga gida neman wani makami.

Mijin ya dau alkawarin maka Teta a kotu har sai an kore shi daga garin sakamakon bibiyar matan mutane da yake.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel