Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 20 a Najeriya

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 20 a Najeriya

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane ashirin (20) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Juma'a, 3 ga Afrilu, 2020.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita ranar Juma'a inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin (20) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 11 a Legas, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun, 1 a Ondo.“

"An samu karin mutane biyu da mutu; 1 a Legas, 1 a Edo."

“Dai-dai Karfe 10:30 na daren 3 ga Afrilu, mutane 210 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami 25 , kuma hudu ya rigamu gidan gaskiya.“

KU KARANTA: Cibiyar NCDC ta saki lambobin jiha-jiha da mutum zai iya kira

Lagos- 109

Abuja - 41

Osun- 21

Oyo- 8

Akwa Ibom- 5

Ogun- 4

Edo- 6

Kaduna- 4

Bauchi- 3

Enugu- 2

Ekiti- 2

Rivers-1

Benue- 1

Ondo - 1

KU KARANTA: An sake sallaman mutane 4 bayan sun warke daga cutar Coronavirus

Mutumi mai shekaru 55 a duniya da ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas LUTH, Idi Araba, sakamakon cutar Coronavirus bai fadawa ma'aikatan kiwon lafiya gaskiyar abinda yake fama da shi ba lokacin da aka kai shi asibiti.

Majiya a asibitin ya bayyana cewa sai bayan mutuwarsa aka gudanar da gwaji aka gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus a jikinsa.

Hakazalika masu jinyarsa suka ki bayyanawa asibitin ainihin abinda ke damunsa da kuma irin tafiye-tafiyen da yayi zuwa kasar waje a makonni baya-bayan nan.

"Amma bayan mai rijistan asibitin ya bayyana masa abubuwan da suka gano a jikinsa, mutumin ya bayyana gaskiyar cewa lallai da yiwuwan ya kamu da cutar COVID-19 saboda tafiyar da yayi kasar waje."

"Ya bayyana cewa tun lokacin da ya dawo daga kasar Holan makonni biyu da suka shude yake fama da tari." Cewar majiyar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel