Yanzu-yanzu: An samu bullar coronavirus na farko a jihar Ondo

Yanzu-yanzu: An samu bullar coronavirus na farko a jihar Ondo

- An samu mutum na farko mai dauke da coronavirus a jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya

- Gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ne ya bayyana labarin a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 3 ga watan Afrilu

- A cewar gwamnan, an fara bibiyar dukkan mutanen da suka yi cudanya da wanda ya kamu da cutar

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sanar da cewa an samu mutum na farko mai dauke da kwayar cutar ta Covid-19 a jiharsa.

Gwamnan ya bayar da sanarwar ne ta shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 3 ga watan Afrilun 2020.

Gwamnan ya ce, "Mun samu tabbacin cewa an samu mutum na farko mai dauke da kwayar cutar covid-19 a jihar Ondo a yammacin yau. An killace wanda ya kamu da cutar a halin yanzu kuma za a bashi kulawa. Mun dauku dukkan matakan da suka dace domin gano wadanda suka yi cudanya da shi kuma za mu rika aike tare da hukumar NCDC."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Legas

Sahara Reporters ta ruwaito cewa mutumin na farko da ya kamu da cutar da coronavirus a jihar ta Ondo jami'in soja ne dan Najeriya da ya dawo daga Indiya a baya-bayan nan.

Wata majiya ta shaidawa wakilin Saharareporters cewa an aike wa jihar sakamakon gwajin ne bayan sun an dauki abin gwaji a jikin mutanen an tura dakin gwaje-gwaje a jihar Osun.

Ya ce, "Akwai mutane biyu da muka zargin suna dauke da kwayar cutar a ranar Laraba. Daya daga Ile Oluji a Okeigbo na biyun kuma soja ne daga 32 Artillery Brigade na rundunar sojojin Najeriya a Barikin Akure.

"Nan take aka dauki abin gwaji daga jikinsu aka aike da shi zuwa Ede a jihar Osun domin yin gwaji, sakamakon ya nuna mutumin na biyu yana dauke da cutar."

A yayin da ya ke sanar da bullar cutar a jihar, Gwamna Akeredolu ya bukaci mutane su kwantar da hankulansu inda ya kara da cewa tuni an tafi da mutumin wurin da za a killace shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel