Coronavirus: Za a kwaso 'yan Najeriya da ke kasashen waje

Coronavirus: Za a kwaso 'yan Najeriya da ke kasashen waje

Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta umurci dukkan ofishin jakadancin ta a kasashen duniya su fara tattara sunayen 'yan Najeriya da ke son dawo wa gida kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Shugaban, Hukumar 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce an dauke wannan matakin ne sakamakon kiraye-kiraye da wasu 'yan Najeriya da ke kasanshen waje ke yi.

Sai dai ta bayyana cewa hukumar ta ce wadanda ke son dawowa gidan ne za su biya kudin jigilar dawo da su kuma za su mika kansu a killace su na tsawon makonni biyu idan sun dawo kasar.

Coronavirus: Za a kwaso 'yan Najeriya da ke kasashen waje

Coronavirus: Za a kwaso 'yan Najeriya da ke kasashen waje
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An rufe masallacin da matasa suka yi wa jami'an yaki da coronavirus rajamu (Hotuna)

Sanarwar da shugaban sashin hulda da al'umma na hukumar NIDCOM, Abdur-Rahman Balogun ya fitar ta ce duk wani dan Najeriya da ke son ya dawo gida ya tuntubi ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar da ya ke zaune.

"Ana shawartar duk wani dan Najeriya da ke kasar waje kuma ya ke son dawowa gida ya sanar da ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar da ya ke su kuma za su tattara sunayen su mika wa ma'aikatar harkokin kasashen waje.

"Hakan yasa Hon. Abike Dabiri-Erewa ta ke kira ga 'yan Najeriya da suke kasashen waje kuma suke da niyyar dawowa gida su yi amfani da wannan damar da gwamatin tarayya ta bayar su sanar da ofisoshin jakandancin Najeriya da ke kasashen da suke zaune."

The Punch ta ruwaito cewa wasu kasashen duniya da suka hada da Birtaniya, Amurka, Isra'ila da wasu kasashen da ke kungiyar tarayyar turai sun fara kwashe 'yan kasar su da ke Najeriya karkashin tsarin kar ta kwana da gwamnatin tarayya ta tanada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel