Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Legas

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Legas

Gobara ta lashe shagunan da ke Maolla Shopping Mall a kasuwar Ebute Ero da ke Idumota a jihar Legas.

The Punch ta ruwaito cewa ba a san ainihin abinda ya yi sanadin gobarar da ta kone shaguna masu lamba 35 da 36 a kasuwar a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce masu kai tallafin gaggawa sun ci karfin wutar kuma babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Legas
Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a kasuwar Legas
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An rufe masallacin da matasa suka yi wa jami'an yaki da coronavirus rajamu (Hotuna)

Ya ce, "Da isar masu taimakon gaggawar, an gano cewa wutar ya tashi ne daga wani rukununin shaguna ta Maola Shopping Mall amma ba'a gano abinda ya yi sanadin gobarar ba.

"Jami'an LASEMA daga yankin Legas ta tsakiya (Sari Iganmu) da jami'an hukumar kashe gobara da 'yan sanda sun yi nasarar kashe gobarar kuma saman ginin ne shaguna masu lamba 35 da 36 ne gobarar ta shafa.

"Masu taimakon gaggawa sun kashe wutar sun koma ofishinsu."

A wani rahoton, kunji cewa an an kashe wani kansilar karamar hukuma a jihar Anambra, Chukwuebuka Ikeji a kan rikicin fili.

Sakamakon hakan, fusatattun matasa a unguwar sun hada kai sun kone gidan Emmanuel Ukandu wanda ake zargi da kashe kansilar.

Har wa yau, matasan sun kuma kona motar bus mallakar Emmanuel Ukandu da ake zargin da ita ya kashe kansilar.

Lamarin ya faru ne a garin Umunna, Umuchukwu a karamar hukumar Orumba ta Kudu na jihar ta Anambra.

An gano cewa Ukandu wanda suka samu rashin jituwa da mammacin saboda fili ya yi amfani da motarsa ne ya nike shi duk da gargadin da yaron motarsa ya masa kan afkuwar hakan.

Mai magana da yawun rundunar tsaro ta NSCDC a jihar, Edwin Okadigbo ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin.

Ya ce an sanar da ofishin NSCDC na Orumba ta Kudu afuwar lamarin a ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel