Yan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun halaka mutane 6

Yan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun halaka mutane 6

Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun tare babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano a jahar Borno inda suka kashe fasinjojin wasu motoci guda biyu kirar Bus, har guda 6 a wani harin kwantar bauna da suka kai musu.

Jaridar Premium Times ta ruwaito wani jami’in kungiyar yan sa kai watau Civilian JTF, CJTF, mai suna Danbatta Bello ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace daya daga cikin motocin mallakin kamfanin sufurin jahar Borno ce, watau Borno Express.

KU KARANTA: Annobar Corona: Dan majalisar Bauchi ya sadaukar da albashinsa N476,000 domin yaki da cutar

Yan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun halaka mutane 6

Yan Boko Haram sun kai ma matafiya harin kwantan bauna, sun halaka mutane 6
Source: Twitter

A cewarsa lamarin ya faru ne da yammacin lahadin da ta gabata yayin damotocin biyu su ke kan hanyarsu ta zuwa Damaturu, inda suka kashe wasu fasinjoji maza guda 6, sa’annan suka tattara sauran mata da kananan yara suka yi awon gaba da su.

Bello ya kara da cewa jami’an tsaro sun samu labarin harin, amma cikakken labarin bai bayyana ba sai a ranar Laraba, ranar da direban motar ya tsere daga hannun miyagun ya dawo gida.

“Direban ya fada mana cewa yan ta’addan sun sa shi ya tuka motar tsawon awanni da dama zuwa tsakiyar daji har cikin dare har zuwa lokacin da man motarsa ta kare, yace a daidai Katapilla Bini a kan hanyar Alagarno motarsa ta tsaya da misalin karfe 3 na dare.

“Daga nan sai yan bindigan suka fada ma direban cewa da shi da matan da kananan yaran su tabbata sun san inda dare ya musu, idan kuma ba haka wasu tawagar Boko Haram za su kashe su idan suka gansu.

“Daga nan direban ya jagoranci matan da kananan yaran a kasa har sai da suka kai wani shingen binciken ababen hawa na Sojoji a Njimtilo, garin Maiduguri, bayan direban ya fada mana abinda ya faru, nan da nan muka zarce zuwa inda lamarin ya ajiye yan Boko Haram din, muka dauko motar.” Inji shi.

Daga karshe Danbatta yace tuni sun mika matan da kananan yaran ga iyalansu, yayin da motar kuma suka mika ta ga hukumar Yansandan jahar Borno.

Shi ma Sale Habib, dan uwan guda daga cikin wadanda abin ya shafa ya bayyana cewa yan ta’addan sun kashe dan uwansa Bakari Abuna, yayin da yan uwansa maza biyu kuma suka jikkata, daya harbin binciga a wuyansa, daya kuma adda aka sara masa, haka zalika mata da kananan yara 5 duk yan uwansa ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel