Matar da ta kamu da Coronavirus ta arce daga wajen magani ta sha alwashin gogawa duk wanda yayi kokarin kama ta

Matar da ta kamu da Coronavirus ta arce daga wajen magani ta sha alwashin gogawa duk wanda yayi kokarin kama ta

- Wata mata wacce ake zargin tana dauke da cutar coronavirus ta tsere daga asibiti

- A bidiyon da ya bazu a yanar gizo, an ga 'yan sanda na bin matar har suka kama ta

- A take kuwa ta watsa musu ruwa daga kofi sannan ta dinga watsa musu yawunta don su bar ta ta cimma burinta na gudu

Wata mata wacce ake zargin tana dauke da cutar coronavirus ta gudu daga asibiti. Bayan da 'yan sanda suka bibiyeta, ta ki basu hadin kai inda ta watsa musu ruwa tare da watsa musu miyau.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, bidiyon ya bazu a yanar gizo. 'Yan sandan Chile ne a bidiyon suke tsere da wata mata mai shekaru 26. A lokacin da suka kama ta, ta watsa musu wani ruwa daga kofi sannan ta watsa musu miyau tare da zaginsu.

Daga bisani dai an kama ta sannan aka saka mata ankwa.

A wani labari na daban.

Wani mutum mai dauke da muguwar cutar coronavirus ya tofa wa wani yawu a fuska yayin da suke hawa jirgi tare a kasar Thailand.

Wani bidiyo wanda na'urar nadar sauti tare da hotuna ta dauka a wani jirgin kasa a Bangkok ya ba mutane mamaki.

A bidiyon, an ga mutum mai fama da cutar coronavirus yana takawa zuwa wurin wani mutum inda ya siya tikiti. A take kuwa ya watsa mishi miyau a fuska.

Mai dauke da cutar coronavirus din mai suna Anan Sahoh dan shekaru 56 ne a duniya. Daga karshe kuwa ya mutu a bandakin jirgin kasan wanda ke tafiya zuwa Narathiwat, kamar yadda jaridar Metro UK ta bayyana. Jami'an kiwon lafiya ne suka duba shi inda suka tabbatar da cewa yana dauke da cutar coronavirus.

Sauran fasinjojin sun ce yana tari da amai a jirgin duk da kuwa ya yi gwajin dole kafin shiga jirgin.

A halin yanzu, hukumomi a kasar Thailand na neman mutumin da ya watsa wa yawun a fuska amma har yanzu babu amo balle labarin shi.

KU KARANTA: Tashin hankali: Budurwa ta kashe saurayinta ta kuma yanke masa mazakuta

Daraktan hukumar jiragen kasa ta Thailand, Thakoon Intrachom, ya ce: "Duk muna cikin damuwa a kan mutumin da aka watsa wa yawu. Da farko dai mun sa 'yan sandan cikin jirgin neman shi amma har yanzu shiru."

"Muna sanar da jama'a cewa in har ka san wani ya watsa maka miyau a fuska ko ka ji labarin wanda aka yi wa haka, a gaggauta mika shi asibiti." Ya ce.

Likitoci sun ce Anan Sahoh ya dawo ne daga Pakistan kuma ya mutu ne filin jirgi na Suvarnabhumi. Dukkan binciken da ake yi a wurare, basu bayyana Anan bashi da lafiya ba.

Amma kuma ya fara tari da amai yayin da ake kan hanya. Bayan duba shi da aka yi, sai jami'an kiwon lafiya suka shawarce shi da ya huta a filin jirgin kasa na Hua Hin don dumin jikinshi dai-dai yake, amma sai ya ce yafi so ya ci gaba da tafiyar shi.

Wajen karfe 10:15 na dare ne aka ga gawarshi a kusa da bandakin jirgin kasan bayan an isa yankin Prachup Khiri Khan.

Tuni kuwa aka yi mishi gwaji kuma aka gano yana dauke da muguwar cutar coronavirus da kuma ciwon suga.

Tuni aka kwashe fasinjoji da ke tare da shi da kuma ma'aikatan jirgin biyu, mai gadi da kuma wani dan sanda don killacewa.

Bayan mutuwar Anan, an yi wa jirgin feshi sannan an shawarci sauran fasinjoji da su kauracewa mutane na kwanaki 14.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel