Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 4 bayan sun warke daga cutar Coronavirus
- Tabarkallah! Mutane hudu sun sake warkewa da muguwar cutar Coronavirus da ta addabi duniya
- Gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa sun sallami marasa lafiyan a ranar Juma'a
Gwamnatin jihar Legas ta alanta sallamar karin masu fama da cutar Coronavirus 4 daga asibitinta .
Gabanin yanzu, an sallami mutane 18 bayan an tabbatar da sun warke daga cutar. A yanzu, babu wanda ya mutu a jihar Legas kuma mutane 22 cikin 98 da suka kamu da cutar sun warke.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: An samu karin masu cutar Coronavirus 20 a Najeriya
Bayan haka, Wani mutumi mai shekaru 55 a duniya ya mutu a asibitin koyarwan jami'ar jihar Legas LASUTH, Idi Araba, sakamakon cutar Coronavirus. Punch ta ruwaito.
A cewar Punch, Majiya a asibitin ya bayyana cewa sai bayan mutuwarsa aka gudanar da gwaji aka gano cewa yana dauke da cutar Coronavirus a jikinsa.
Yace: "An gudanar da gwajin garkuwar jiki ta alamar yatsu kuma na tabbatar da cewa yana da cutar COVID-19."
Ya kara da cewa mutumin wanda ya kasance yana fama da cutar koda ya kwanta a asibitin ne ranar Alhamis.
Amma masu jinyarsa suka ki bayyanawa asibitin ainihin abinda ke damunsa da kuma irin tafiye-tafiyen da yayi zuwa kasar waje a makonni baya-bayan nan sai bayan mutuwarsa.
Majiya ya cigaba da cewa: "Mutumin bai bayyana tafiye-tafiyen da yayi ba ko kuma kila ya hadu da wani wanda yayi tafiya kasar waje ba."
"Ya fadawa likitoci cewa ba ya fama tari, wahalar numfashi, ciwon gabobin jiki ko gudawa."
"Amma bayan mai rijistan asibitin ya bayyana masa abubuwan da suka gano a jikinsa, mutumin ya bayyana gaskiyar cewa lallai da yiwuwan ya kamu da cutar COVID-19 saboda tafiyar da yayi kasar waje."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng