An bindige, Charles Tambe, mai tsaron gidan Abia Warriors a Ibadan

An bindige, Charles Tambe, mai tsaron gidan Abia Warriors a Ibadan

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun harbi mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Abia Warriors, Charles Tambe a birnin Ibadan da ke jihar Oyo kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

An gano cewa an garzaya da Tambe zuwa asibiti mai suna University College Hospital (UCH) da ke Ibadan domin samun kulawan likitoci.

Kungiyar ta Abia Warrior, a shafinta na Twitter, @AbiaWarriors ta wallafa afkuwar labaran mara dadin ji inda ta ce:

"Wasu 'yan daba sun harbi mai tsaron gidan kungiyar mu, Charles Tambe a safiyar yau a Ibadan. Tambe yana asibiti a UCH a Ibadan yana samun kulawa. Mahukuntan kungiyar mu suna bin dididgin abinda ya yi sanadin afkuwar lamarin. Za mu cigaba da yi muku bayanin abinda ke faruwa. Muna bawa kowa shawarar ya guji afkawa cikin fitina."

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanin asibitoci a Jalingo da Calabar

A halin yanzu dai babu cikakken bayani a kan abinda ke faruwa a gasar Premier ta Najeriya da ya haifar da hakan a lokacin da ake rubuta wannan rahoton.

Ku cigaba da kasancewa da mu domin samun cikakken rahoton ...

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel