Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa Gwamna Sanwo-Olu ya fito

Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin coronavirus da aka yi wa Gwamna Sanwo-Olu ya fito

- Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa sakamakon gwajin covid-19 da aka yi wa gwamnan jihar ya nuna cewa Babajide Sanwo-Olu bai kamu da cutar ba

- Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi ya ce gwamnan da matarsa da 'ya'yansa duk ba su kamu da kwayar cutar ba

- Kwamishinan ya kara da cewa hadiman gwamnan da na matarsa dukkansu babu wanda ya kamu da kwayar cutar da covid-19

Kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu bai kamu da coronavirus ba kamar yadda sakamakon gwajin da aka yi masa ya nuna.

Kwamishinan lafiyar ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 3 ga watan Afrilun 2020 a Twitter.

Ya ce matar gwamnan da 'ya'yansu da hadimansu duk suma an musu gwajin kuma babu wanda ke dauke da kwayar cutar a cikinsu.

Kwamishinan ya ce, "Ina farin cikin sanar da cewa gwajin kwatar cutar covid-19 da aka yi wa kwamandan yaki da cutar na Legas, Gwamna Babajide Sanwo-Olu @jidesanwoolu da matarsa @jokesanwoolu da 'ya'yansu har ma da hadimansu ya nuna cewa dukkan su ba su kamu da cutar ba."

DUBA WANNAN: Coronavirus: Najeriya ta yi nadamar rokon na'uarar 'ventilator' daga attajirin Amurka

Abayomi ya mika godiyarsa da mazauna jihar Legas bisa goyon bayan da suka bayarwa wurin yaki da cutar. Ya kuma bukaci al'ummar jihar su cigaba da kiyaye dokokin da masana lafiya suke bayar na guje wa cinkoso, wanke hannu da sauransu.

Gwamnan da ya tabbatar da sakamakon gwajin nasa a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a 3 ga watan Afrilu ya ce yana da muhimmanci ya yi gwajin ya san matsayinsa saboda ya mayar da hankalinsa wurin aikinsa na yi wa jihar hidima.

Gwamnan ya ce, "A matsayinna na shugaba da ya san ya kamata, yana da muhimmanci in yi gwajin na covid-19 domin in tabbatar babu abinda zai dauke min hankali a wurin yi wa Legas jagoranci a wannan lokacin. Ina farin cikin sanar da ku cewa sakamakon gwajin ya nuna ba na dauke da cutar. Matata da yara ne suma ba su dauke da cutar."

A wani rahoton, Cibiyar kiyaye yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta tabbatar da sabbin mutane 10 da suka kamu da kwayar cutar wanda hakan ke nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 184.

Hukumar ta NCDC a shafin ta na Twitter a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilu ta bayyana cewa an samu sabbin mutane 7 da suka kamu da cutar a Legas yayin da aka samu wasu uku a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel