Coronavirus: Atiku ya gargadi al'umma game da wata damfara da ake yi da sunansa

Coronavirus: Atiku ya gargadi al'umma game da wata damfara da ake yi da sunansa

Atiku Abubaktar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya karyata cewar ya bude shafin intanet inda ya ke tattara bayannai na al'umma da zai yi amfani da shi domin raba musu kudi a matsayin tallafi sakamakon bullar coronavirus.

Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Paul Ibe ne ya ce al'umma su yi watsi da wata sanarwa da ke yawo a dandalin sada zumunta da ke cewa mutane su bayar da bayyanan su kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ibe ya ce wasu 'yan damfara ne suka kirkiri sakon da nufin damfarar 'yan Najeriya inda suke amfani da shafi mai lakabin - www.atikufoundation.online - da ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar bai san da shi ba.

Damfara ce: Atiku ba ya karbar bayyanan mutane domin raba musu kudi
Damfara ce: Atiku ba ya karbar bayyanan mutane domin raba musu kudi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce, "Muna son mu sanar da 'yan Najeriya cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba shi da wata alaka da wani sako da ke yawo a dandalin sada zumunta da ke umurtar mutane cewa su ziyarci wani shafin intanet.

"Muna sanar da al'umma cewa duk wani shafi da aka bude na neman bayyanan sirri na 'yan Najeriya domin ba su tallafin kudi karya ne kuma yaudara ce.

"Wasu 'yan damfara ne kawai suke son su cuci 'yan Najeriya, ta hanyar karbar bayyanan sirri su domin wata manufa na su mara kyau a shafukan sada zumunta.

"Atiku Abubakar bai san da wannan batun ba na bayar da tallafi da aka ce za a bayar da wannan shafin https//www.atikufoundation.online, da 'yan damfara ke tura wa al'umma da sunan sa.

"A matsayinsa na dan kasa mai kishin kasar sa, Wazirin Adamawa ya yi alkawarin bayar da tallafinsa ga gwamnatin tarayya ta hannun Priam Support Group domin taimakawa gwamnatin wurin yaki da cutar coronavirus da ta zame wa duniya annoba."

Ibe ya bukaci hukumomin tsaro su bincika su gano 'yan damfarar da suka kirkiri sakon domin su hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel