Yanzu-yanzu: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan daya

Yanzu-yanzu: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan daya

Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a fadin duniya ya zarce miliyan daya a kasashe 181 cikin watanni uku.

Lissafi daga jami'ar Johns Hopkins dake kasar Amurka da ke bibiyan yawan mutane ya nuna cewa mutane 1,002, 159 ne suka kamu da cutar kawo yanzu.

Hakazalika, mutane 208, 949 suka samu warkewa daga cutar bayan jinya a asibiti. Amma mutane 51, 945 sun rigamu gidan gaskiya.

Kasashen da ke kan gaba wajen yawan masu cutar sune:

Amurka - 236,339 US

Italiya - 115,242 Italy

Spain - 110,238

Jamus - 84,600

Sin - 82,432

Faransa - 59,929

Iran - 50,468

Birtaniya 34,164

KU KARANTA An sallami mutane 11 daga asibiti a Legas bayan sun warke daga Coronavirus

Yanzu-yanzu: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan daya
miliyan daya
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin kasar Jamus ta dauki alwashin baiwa Najeriya tallafin makudan Yuro miliyan 5.5, kimanin naira biliyan 2.2 kenan a matsayin tallafinta sakamakon bullar annobar Coronavirus a kasar.

Punch ta ruwaito ofishin kula da walwalar jama’a a Najeriya ce ta tabbatar da haka, inda tace ofishin jakadancin Jamus a Najeriya ce ta yi wannan alkawari, a daidai lokacin da kasashen nahiyar Afirka ke fama da annobar.

Ofishin kula da walwalar jama’an ta sanar da taimakon ne a shafinta na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ta ce tallafin zai taimaka wajen kulawa da talakawa marasa karfi da abinci, ruwan sha da kuma matsuguni.

A bangare guda kuwa, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta janye rokon da Ma'aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren kasa ta yi na neman tallafin na'uarar taimakawa numfashi ta 'ventilator' daga wurin attajirin kasar Amurka, Elon Musk domin yi wa masu fama da cutar coronavirus magani a Najeriya.

Mai kamfanin SpaceX kuma babban injiniyan kamfanin, Musk, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamisa cewa kamfaninsa tana da raran na'urorin taimakawa numfashin da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na Amurka (FDA) suka amince da ingancinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel