Coronavirus: Na gano maganin ta - Farfesan Najeriya

Coronavirus: Na gano maganin ta - Farfesan Najeriya

Shugaban Luminar International College of Alternative Medicine da ke Enugu, Farfesa Joseph Akpa ya ce ya gano maganin kwayar cutar covid-19 da ta zama annoba a duniya.

Farfesa Akpa ya yi wannan ikirarin ne yayin taron manema labarai da aka yi a Enugu a ranar Laraba kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, tuni ya riga ya kirkiri magungunan kara kuzarin jiki da za su inganta garkuwar jiki da kuma wasu da za su kashe kwayar cutar domin tabbatar da cewa mutum ya warke dari bisa dari.

Ya kuma kallubalanci asibitoci su kawo masa duk wani da aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar domin ya yi masa magani.

Coronavirus: Wani farfesa a Najeriya ya ce ya gano magananin cutar
Coronavirus: Wani farfesa a Najeriya ya ce ya gano magananin cutar
Source: Twitter

Ya ce: "Ina kallubalantar duk wata cibiyar lafiya ko asibiti ta kawo min majiyanci da aka tabbatar yana dauke da kwayar cutar coronavirus a ga yadda zai warke cikin kwanki kadan.

DUBA WANNAN: Coronavirus: An jefi jami'an tsaron gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma

"Idan sakataren dindindin na jihar Enugu ko Ma'aikatar Lafiya na jihar suke tuntube ni domin in yi wa wani da ya kamu da cutar magani zan yi maganin ba tare da na saka musu wasu ka'idoji ba."

"Ina yi wa Allah Godiya da ya yi amfani da ni domin gano maganin cutar da ke dab da halaka mutanen duniya baki daya," in ji shi.

Farfesa Akpa ya ce yunkurin da 'yan kasar China da wasu ke yi na ganin sun fi sauran jinsin myutane daraja ne ne ya janyo barkewar cutar.

Ya yi ikirarin cewa 'yan kasar China suna amfani da wasu hanyoyi ta yadda kuruwan su ke fita daga jikinsu ya tafi wasu duniyoyin domin nemo wasu sirri su dawo da shi duniyar mu.

Daga karshe ya fada wa manema labaran cewa zai basu kwallaben sinadarin maganin kara karfin garkuwan jiki kana zai koyar da su wasu dabi'u na kare kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel