Da duminsa: Likita ya kamu da Coronavirus daga jikin mara lafiya a Edo

Da duminsa: Likita ya kamu da Coronavirus daga jikin mara lafiya a Edo

Shugaban kungiyar likitoci a Najeriya, Aliyu Sokomba, ya ce daya daga cikin mambobin kungiyarsa mai jinyar masu cutar Coronavirus ya kamu da cutar daga jikin mara lafiya.

Sokomba a hirar da yayi da tashar Channels TV ranar Alhamis ya ce likitan ma'aikaci ne a asibitin koyarwan Irrua dake jihar Edo.

Ya ce wajibi ne a rika lura da ma'aikatan kiwon lafiya dake jinyar masu cutar Coronavirus da zazzabin Lassa muddin kasar na son cigaba.

Yace: "A yanzu, ma'aikatan kiwon lafiya na iyakan kokarinsu ta hanyar takaita yaduwar cutar amma su rayukansu na cikin hadari,"

"Daya daga cikin ma'aikatanmu ya mutu jiya sakamakon zazzabin Lassa. Haka rayuwan ma'aikatan kiwon lafiya ya koma a kasar nan."

"Dakta Philip Dzunan ne likita na shida da zai mutu sakamakon zazzabin Lassa a kasar nan kuma babu abinda akeyi don kiyaye hakan."

"A jiya kuma, daya daga cikin Likitocinmu dake ISTH Iruaa, ya kamu da cutar COVID-19. Hakan na nufin cewa kawai ana barin likitocin na kamuwa da cutar kuma babu wanda ya damu da su."

"Babu inshoran da aka shirya musu, babu la'ada. Kai abinda likitocin nan ke samu a karshen wata na alawus N5000 ne."

Wannan ya biyo bayan zanga-zangar da kungiyar ma'aikatan jinya da ungumomin Najeriya ta gudanar ranar Laraba kan rashin kayayyakin kiyaye kansu daga kamuwa da wadannan cututtuka.

Da duminsa: Likita ya kamu da Coronavirus daga jikin mara lafiya a Edo

Da duminsa: Likita ya kamu da Coronavirus daga jikin mara lafiya a Edo
Source: UGC

A wani labari daban, Gwamnatin jihar Cross River ta tuhumci jami’an hukumar yan sandan Najeriya da laifin yiwa yunkurin da gwamnatin jihar keyi na hana cutar Coronavirus shiga jihar zagon kasa ta hanyar amsan cin hanci wajen masu kokarin shiga.

A wani jawabi, hadimin gwamna Ben Ayade, Peter Iyali, ya bayyana cewa yan sandan da aka zuba iyakokin jihar na karban cin hancin N500 hannun matafiya kuma suna bari suna shiga.

Yace wannan abu da bata gari cikin yan sanda ke yi a hanyar Calabar-Itu abin kunya ne kuma zagon kasa ne ga kokarin da gwamnatin jihar keyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel