An rufe masallacin da matasa suka yi wa jami'an yaki da coronavirus rajamu (Hotuna)

An rufe masallacin da matasa suka yi wa jami'an yaki da coronavirus rajamu (Hotuna)

Mahukunta a karamar hukumar Agege da ke jihar Legas sun yi nasarar rufe babban masallacin unguwar ta Agege saboda saba dokokin da gwamnatin jihar ta saka ha hana cinkoso a wurare domin kare yaduwar kwayar cutar covid-19 da aka fi sani da coronavirus da ke yaduwa a jihar.

An kuma yi amfani da wannan damar wurin yi wa masallacin feshin magani kamar yadda kakakin gwamnan jihar Legas Gboyega Akosile ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Wannan ya biyo bayan hargitsi da ya faru a masallacin ne a jiya inda wasu jami'an kwamitin wayar da kan mutane kan yaduwar coronavirus suka tafi masallacin domin fadakar da al'umma amma aka yi musu ruwan duwatsu.

DUBA WANNAN: An kashe kansilar karamar hukuma saboda rikicin fili

A baya mun kawo muku cewa masallatan da adadin su ya dara 250 sun kai wa jami'an kwamitin kar ta kwana na hana yaduwar kwayar cutar Covid-19 na jihar Legas hari a babban masallacin unguwar Agege a yayin da jami'an suka ziyarci masallacin domin tabbatar da cewa mutanen suna bin dokar da gwamnatin jihar ta saka.

A wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Twitter @followlasg, gwamnatin jihar Legas ta yi Allah wadai da halin da matasan suka nuna na saba dokar da jihar ta saka tare da yunkurin kai wa jami'an gwamnati hari.

Da ya ke jawabi game da afkuwar lamarin, Shugaban hukumar kiyaye muhalli na Legas (LASEPA) kuma shugaban kwamitin ta ko ta kwanan, Dr Dolapo Fasewa ya ce mambobin kwamitin da suka kunshi jami'an LASEPA da Kwamitin bayar da agajin gaggawa na Legas sun ga al'ummar sun taru da yawa suna yin sallar Isha'i ne wanda hakan ya saba wa dokar hana fita waje da gwamnatin jihar ta kafa sakamakon yaduwar da kwayar cutar ke yi a jihar.

Ta bayyana cewa matasa musulmi a fusace suna kabbara suka fara kai wa jami'an hari sannan daga bisani wadanda ke cikin masallacin da adadin su ya kai 300 suka fito suna kabbara suka fara jifar motar jami'an hukumar.

Amma daga bisani 'yan sanda sun taimaka sun dakatar da hare-haren tare da tabbatar da cewa ba a yi wa jami'an su rauni ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel