Yan bindiga sun kashe mutane 22 a Sakkwato, sun banka ma gidaje wuta da dama
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai wata mummunan hari a kauyen Gangara dake cikin karamar hukumar Sabon Birni ta jahar Sakkwtao inda suka kashe mutane 22 tare da kona kadarori da dama.
Daily Trust ta ruwaito wasu mazauna kauyen da suka shaida harin da idanuwansu sun bayyana cewa baya ga kisan kiyashi da yan bindigan suka yi ma jama’ansu, sun kuma raunata wasu da dama, sa’annan wasu sun bace har yanzu ba’a san inda suke ba.
KU KARANTA: Na dauki babban darasi daga kamuwa da Coronavirus – Babandede, shugaban Immigration
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an garzaya da wadanda suka samu raunin zuwa asibiti domin samun kulawa, yayin da wadanda suka rasa rayukansu a dalilin harin kuwa an gudanar da jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ta tanadar.
Wani mai suna Laminu Umar ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yan bindigan suka kai ma kauyen hari a duk tsawon lokaci da aka dade ana kai hare hare a yankin sakamakon sun sha yin kokarin kai harin amma Allah na karewa.
“Sun sha yin kokarin kai hari kauyenmu, amma jama’a na mayar dasu, muna tunanin sun gayyaci abokansu daga wasu jahohi ne da suka basu gudunmuwa wajen kaddamar da wannan harin, hakan ne yasa suka samu nasara.
“Da misalin karfe 3:30 na rana suka kai harin a kan babura 150 dauke da mutane uku uku dukkaninsu dauke da muggana makamai, shigarsu kauyen suka fara yekuwa suna harbin mai kan uwa da wabi suna kashe duk wanda suka gani tare da gona gidaje da motoci.” Inji shi.
Laminu yace yan bindigan sun kwashe tsawon awanni biyu suna cin karensu babu babbaka, daga bisani kumasuka tattara dabbobin dake garin, amma yayin da suka hangi motocin Sojoji sun tunkaro su, sai suka shige cikin daji.
Shi ma kaakakin rundunar Yansandan jahar Sakkwato, DSP Muhammad Sadiq ya tabbatar da harin.
A wani labarin kuma, dakarun rundunonin Sojin kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da wasu sabbin hare hare domin bankado mayakan Boko Haram tare da fatattakarsu daga sabuwar mabuyar da suka koma na tsibirin Tunbuns dake tafkin Chadi.
Jaridar The Nation ta bayyana cewa yan ta’addan sun tsere zuwa tsibirin sakamakon rakiyan Kura da Sojojin Najeriya suka musu daga inda suka saba kaddamar da hare hare a kan fararen hula mazauna kauyukan yankin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng