Hotunan ganawar da Buhari ya yi da kwamitin kar ta kwana na yaki da Covid-19 a Abuja

Hotunan ganawar da Buhari ya yi da kwamitin kar ta kwana na yaki da Covid-19 a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis 2 ga watan Afrilun 2020 ya gana da mambobin kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa a kan yaki da annobar covid-19 wato coronavirus a babban birnin tarayya Abuja.

An yi taron ne domin yin bita a kan yadda bullar annobar ta shafi tattalin arzikin kasar.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da Ministan Kudi, Hajiya Zainab Ahmed, Gwamnan babban bankin kasa (CBN), Mista Godwin Emefiele, Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, shugaban NNPC, Mele Kyari da kuma 'yan kwamitin.

DUBA WANNAN: Covid-19: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi

Bullar annobar ta coronavirus dai ta yi illa sosai ga tattalin arzikin kasashe da dama na duniya wanda hakan ya saka darajar danyen man fetur a kasuwannin duniya ya fadi.

Hakan yana daga cikin dalilan da yasa gwamnatin Najeriya ta rage kudin litar man fetur a kasar daga Naira 145 zuwa Naira 123.

A wani rahoton, mun kawo muku cewea shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da tan 70,000 daga ma'adanar hatsi ta kasa don raba wa mabukata a kasar nan a matsayin hanyar saukaka barnar da cutar coronavirus.

Sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban kwamitin shugaban kasa a kan COVID-19, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi karo na uku na PTF a ranar Laraba.

Kamar yadda yace, tan 60,000 sau dubu na hatsi za a raba ne a jama'ar jihohi birnin tarayya, Legas da jihar Ogun. Sauran tan 10,000 sau dubu din kuwa za a raba ne ga mabukatan da ke sauran jihohin Najeriya.

Gwamnatin ta dauki wannan matakin ne domin saukaka wa al'umma matsatsin da suka shiga sakamakon saka dokar ta baci a wasu johohi domin takaita yaduwar covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel