Bayan rufe iyakokin jiha, Yan sanda na karban cin hancin N500 hannun matafiya - Gwamnatin Ayade

Bayan rufe iyakokin jiha, Yan sanda na karban cin hancin N500 hannun matafiya - Gwamnatin Ayade

Gwamnatin jihar Cross River ta tuhumci jami’an hukumar yan sandan Najeriya da laifin yiwa yunkurin da gwamnatin jihar keyi na hana cutar Coronavirus shiga jihar zagon kasa ta hanyar amsan cin hanci wajen masu kokarin shiga.

A wani jawabi, hadimin gwamna Ben Ayade, Peter Iyali, ya bayyana cewa yan sandan da aka zuba iyakokin jihar na karban cin hancin N500 hannun matafiya kuma suna bari suna shiga.

Yace wannan abu da bata gari cikin yan sanda ke yi a hanyar Calabar-Itu abin kunya ne kuma zagon kasa ne ga kokarin da gwamnatin jihar keyi.

Yace: “Muna bukatan kowa ya yi la’akari da irin halin da muke ciki. Yan sanda suyi aikinsu yauzu, kila idan wannan annobar ta wuce, zasu iya komawa halinsu da suka shahara da shi.”

“Wannan baa bun wasa bane. Idan yan sanda basu shirya taimakawa gwamnati ba, za’a ciresu daga iyakokin jihar kuma a baiwa matasa ikon tabbatar da dokar hana shigan.”

“Yanzu cikin mutane 17 da aka yiwa gwaji a jihar Akwa Ibom, an tabbatar biyar sun kamu, jihar Cross River na cikin matsala sakamakon halin bata garin jami’an tsaro masu amsan cin hanci.”

“Wannan abun ta shiga jihohin dake makwabtaka damu; Akwa Ibom da Benue. Yanzu Cross River na cikin hadari.”

Martani kan lamarin a madadin kwamishanan yan sandan jihar, Mr Uche Anozia, mataimakin kwamishanan Cletus, yace babu gaskiya cikin zargin da ake yi musu.

Bayan rufe iyakokin jiha, Yan sanda na karban cin hancin N500 hannun matafiya - Gwamnatin Ayade

Yan sanda
Source: Twitter

Source: Legit

Tags:
Online view pixel