Saurayi ya harbe budurwarshi sannan ya harbe kanshi kan ya rasa aikin yi saboda Coronavirus

Saurayi ya harbe budurwarshi sannan ya harbe kanshi kan ya rasa aikin yi saboda Coronavirus

- Wani dan kasar Amurka ya matukar fusata da annobar coronavirus da kuma rasa aikin shi da yayi sakamakon ta

- Kamar yadda shaidu suka bayyana, ya dau bindiga ne inda ya harbi budurwarshi sannan ya kashe kanshi daga bisani

- An yi nasarar ceto ran budurwar a asibiti amma kuma shi ya rasa ran shi sakamakon harbin kanshi da yayi a kirji

Wani dan asalin kasar Amurka da ya matukar fusata bayan ya rasa aikin shi sakamakon annobar coronavirus, ya harba budurwarshi kuma daga bisani ya kashe kanshi.

Hukumomi sun ce an kira su ne daga gidan shi da ke Wilson Borough, mai nisan mil 70 daga arewa maso gabas din Philadelphia, wajen karfe 1:20 na ranar Litinin. An bayyana yadda aka ji tashin karar bindiga.

A lokacin da jami'ai suka isa wurin, sun tarar da Roderick Bliss IV mai shekaru 38 baya numfashi sannan da alamun harbin bindiga. An kuma ga wata karamar bindigar fiston a tare da gawar.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, kafin ya kashe kan shi, ya harba budurwarshi mai shekaru 43 wacce 'yan sanda suka samu da harbin bindiga a bayanta bata mutu ba. Tuni kuwa aka garzaya da ita asibiti inda aka cire mata harsashin.

KU KARANTA: Lamari ya baci: Kasar Rasha ta fara aikawa da kasar Amurka kayan tallafi saboda cutar Coronavirus

Budurwar ta samu sauki bayan an cire harsashin amma a halin yanzu tana kwance a asibiti.

Matar tare da wasu shaidu sun sanar da 'yan sandan cewa Bliss ya ci gaba da fusata ne tun bayan barkewar cutar coronavirus. Karin fusatar kuwa shine yadda ya rasa aikin shi.

"Ya shiga gidan kasa sannan ya fito rike da bindigar. Ya ce ya yi addu'a kuma sai ya aikata abinda yayi buri. Ya harbeta har sau hudu amma harsashi daya ne ya sameta. Daga nan ne ya harbi kanshi," cewar shaidar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel