Coronavirus: An jefi jami'an tsaron gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma

Coronavirus: An jefi jami'an tsaron gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma

Wasu masallata da adadin su ya dara 25 sun kai wa jami'an kwamitin kar ta kwana na hana yaduwar kwayar cutar Covid-19 na jihar Legas hari a babban masallacin unguwar Agege a yayin da jami'an suka ziyarci masallacin domin tabbatar da cewa mutanen suna bin dokar da gwamnatin jihar ta saka.

A wani rahoto da ta wallafa a shafinta na Twitter @followlasg, gwamnatin jihar Legas ta yi Allah wadai da halin da matasan suka nuna na saba dokar da jihar ta saka tare da yunkurin kai wa jami'an gwamnati hari.

Da ya ke jawabi game da afkuwar lamarin, Shugaban hukumar kiyaye muhalli na Legas (LASEPA) kuma shugaban kwamitin ta ko ta kwanan, Dakta Dolapo Fasewa ya ce mambobin kwamitin da suka kunshi jami'an LASEPA da Kwamitin bayar da agajin gaggawa na Legas sun ga al'ummar sun taru da yawa suna yin sallar Isha'i ne wanda hakan ya saba wa dokar hana fita waje da gwamnatin jihar ta kafa sakamakon yaduwar da kwayar cutar ke yi a jihar.

Coronavirus: An jefi jami'an gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma
Coronavirus: An jefi jami'an gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kungiyar Al-Qaeda ta goyi bayan tsarin killace kai don kare yaduwar annobar coronavirus

Ta bayyana cewa matasa musulmi a fusace suna kabbara suka fara kai wa jami'an hari sannan daga bisani wadanda ke cikin masallacin da adadin su ya kai 300 suka fito suna kabbara suka fara jifar motar jami'an hukumar. Amma daga bisani 'yan sanda sun taimaka sun dakatar da hare-haren tare da tabbatar da cewa ba a yi wa jami'an su rauni ba.

Coronavirus: An jefi jami'an gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma
Coronavirus: An jefi jami'an gwamnatin Legas da suka ziyarci wani masallaci domin fadakar da al'umma
Asali: Twitter

Fasewa ta bayyana cewa mafi yawancin wuraren ibada sun bawa hukumar hadin kai saboda haka ta yi mamakin ganin yadda matasan suka harzuka kuma suka nemi kai wa jami'an ta hari.

Ta ce, "Tawagar mu ta ziyarci wuraren ibada da dama kuma ta wayar wa al'umma kai ta hanyar ba su shawarwarin killace kansu da takaita mu'amula na kusantar juna. Amma a wannan masallacin mutane sunyi yawa sosai. Ta ce nisantar juna yana taimakawa wurin kiyaye yaduwar coronavirus. Mutanen suna jefa rayuwarsu da na makwabtansu cikin hatsari."

Daga karshe ta yi kira ga dukkan mazauna jihar su cigaba da bawa gwamnati hadin kai tare da kiyaye dokokin da aka kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel