Annobar Corona: Ku kama duk wanda kuka ga bai sa kyallen rufe fuska ba – Gwamna ga Yansanda

Annobar Corona: Ku kama duk wanda kuka ga bai sa kyallen rufe fuska ba – Gwamna ga Yansanda

Gwamnan jahar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade ya bayar da umarni ga jami’an tsaron jahar da su tabbata sun kama duk wani mutumin da suka gan shi yana tafiya a kan titi ba tare da yana sanye da kyallen rufe fuska ba.

TheCable ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, inda yace yana so Yansanda su fara dabbaka wannan umarni ne daga ranar Juma’a, 3 ga watan Afrilu, duk kuwa da cewa hukumar kiwon lafiya ta Duniya, WHO, ta bayyana cewa marasa lafiya ne kadai suke bukatar amfani da kyallen, ko kuma masu jinyarsu.

KU KARANTA: Coronavirus ta kashe wani babban likita daga Arewacin Najeriya a kasar Birtaniya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya kaddamar da wannan doka ne duk da cewa ba’a samu bullar cutar Coronavirus a jahar ba, amma ya ce ya dauki wannan mataki ne na dakile yaduwar cutar zuwa jaharsa.

“Sakamakon bullar Coronavirus a makwabtan jahohinmu, gwamnan jahar Ribas, Sir Ben Ayade ya bayar da sabbin umarni ga al’ummahar jahar kamar haka;

“Babu wani mazaunin jahar da za’a yarda ya sake fita wajen gidansa ba tare da ya sanya kyallen rufe fuska ba daga ranar 3 ga watan Afrilu. Duk wanda ya taka wannan doka, tabbas doka za ta taka shi domin kuwa jami’an tsaro za su kama shi, sa’annan a killace shin a tsawon kwanaki 14.

“Gwamnatin jahar ta umarci kamfanin masaka ta jahar ta samar da kyallayen rufe fuska wanda za’a raba ma al’ummar jahar kyauta, amma duk wanda bai samu kyautar kyallen zuwa Juma’a ba, ya tabbata ya sayi nasa kafin karshen wa’adin.

“Duk wani taron jama’a ya haramta, kasuwannci za su cigaba da zama a garkame, amma banda shagunan sayar da abinci. Duk wasu hanyoyin shiga da fita jahar an garkame su, ba zamu bari moto ko mutum ya shigo mana jaha ba ta ko ta wani dalili.” Inji shi.

A wani labari kuma, mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga jama’an jahar Kano su cigaba da bin dukkanin matakan kare kai daga kamuwa da annobar cutar Coronavirus, tare da yin biyayya ga shawarwarin masana kiwon lafiya.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito Sarkin ya bayyana haka ne yayin da yake yi ma al’ummar Kano jawabi a ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu, inda ya koka tare da bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yawaitan cutar a Najeriya.

Sarki ya ce ya umarci dukkanin hakimansa da dakatai da kuma shuwagabannin addinai su cigaba da sa ido a kan jama’a, kuma su kai rahoton duk inda aka samu wani dake dauke da alamomin cutar da basu gane ba ga masana kiwon lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel