Kungiyar Al-Qaeda ta goyi bayan tsarin killace kai don kare yaduwar annobar coronavirus

Kungiyar Al-Qaeda ta goyi bayan tsarin killace kai don kare yaduwar annobar coronavirus

Kungiyar 'yan ta'addan Al- Qaeda wacce ta mayar da hankali wajen kawar da al'adun turawan yamma da gwamnatocin su, sun amincewa da tsare-tsaren Cibiyar Lafiya ta Duniya (WHO) na killace kai a matsayin hanyar yaki da cutar coronavirus a fadin duniya.

A wani jawabi ga manema labarai da kungiyar ta mika ga jaridar HumAngle a ranar Talata, Al-Qaeda ta jawo hankula ne ta hanyar amfani da hadisai wajen nuna wa al'umma abinda ya kamata a yi a yayin barkewar annoba.

Daga cikin hadisan akwai wadanda suka yi magana a kan zama a waje ba tare da bari ba matukar annoba ta barke.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Shugabanmu Annabi Muhammad ya koyar da mu hakuri tare da zama a inda muke yayin da annoba ta barke a wuri. Hakazalika duk wanda ya rasa ransa sakamakon hakan yana da ladar shahidi," a cewar kungiyar.

Coronavirus: Kungiyar Al-Qaeda ta bayyana matsayar a kan killace kai

Coronavirus: Kungiyar Al-Qaeda ta bayyana matsayar a kan killace kai
Source: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Ta kwatanta annobar da jarabawa daga Ubangiji sakamakon rashin adalci da kuntatawa musulmai da gwamnatocin kasashen duniya suke yi.

Al-Qaeda ta dora karayar tattalin arzikin kasashen duniya da rashin amfani da tsarin musulunci da kuma riba da ake amfani da ita a tattalin arzikin kasashe.

ISIS, wata kungiyar ta'addanci wacce ke da akida iri daya da ta Al-Qaeda, ta kwatanta wannan annoba da kokarin Ubangiji wajen tarwatsa kafirai.

Ta yi kira ga 'yan kungiyar da kada su yada makamansu duk da kuwa barkewar annobar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel