Gwamnan Najeriya ya kaddamar da azumin kwanaki 3 saboda Coronavirus

Gwamnan Najeriya ya kaddamar da azumin kwanaki 3 saboda Coronavirus

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya sanar da garkame jaharsa ta kowanne kusurwa domin kare yaduwar cutar Coronavirus a jahar da ma kasa baki daya, kamar yadda rahoton jaridar Sahara Reporters ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Larab, 1 ga watan Afrilu ta bakin mai magana da yawunsa, Donald Ojogo, wanda ya bayyana cewa gwamnan ya hana shiga ko fitar duk wata mota jahar.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana shige da fice

Ga dai yadda sanarwar ta kasance: “Duba da yadda cutar COVID-19 ke yaduwa a Najeriya, gwamnatin jahar Ondo ta bada umarnin kulle iyakokin ta da makwabtanta, musamman jahohin Ekiti, Osun, Kogi, Edo da Elefon.

“Haka zalika mun rufe iyakokinmu ta ruwa da jahohin Ogun da Legas, an yi haka ne domin dakatar da duk wasu sufuri a tsakanin jahohin don gudun kada wasu daga waje su shigo mana da annobar, dokar za ta fara aiki ne daga karfe 6 na daren Alhamis, 2 ga watan Afrilu.

“An tanadi tsauraran matakan tsaro da kuma kwamitin sa ido domin tabbatar da jama’a sun yi biyayya ga umarnin gwamnati a matsayin wani mataki na kariya daga shigar COVID-19 jahar Ondo.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya kaddamar da azumin kwanaki 3 a jahar, sa’annan ya yi kira ga jama’an jahar da su dauki azumin daga ranar Alhamis domin neman taimakon Allah a wannan halin jarabawa da ake ciki.

A wani labarin kuma, wani babban likitan Najeriya, dan asalin jahar Kwara amma mazaunin kasar Ingila, Dakta Alfa Sa’adu ya kamu da annobar cutar Coronavirus, kuma har ta yi ajalinsa a ranar Litinin, 30 ga watan Maris a birnin Landan.

Dakta Sa’ad ya kwashe fiye da shekaru 40 yana aiki da hukumar kiwon lafiya ta kasar Birtaniya, inda har ya taba zama babban likitan birnin Landan gaba daya kafin ya yi murabus daga aiki, amma ya fito daga ritaya domin taimaka ma marasa lafiya masu cutar Corona.

Dan mamacin, Dani Saadu ya bayyana cewa mahaifinsa ya kwashe tsawon makonni biyu yana fama da cutar kafin ta kar shi, kamar yadda ya sanar a shafinsa na dandalin sadarwar zamani na Facebook.

“Yau da misalin karfe 7:30 ne mahaifina Dakta Alfa Saadu ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus, ya kwashe tsawon makonni biyu yana fama da cutar, ma’aikatan NHS sun yi iya bakin kokarinsu don ganin sun ceci rayuwarsa, amma ina, lokaci yayi.

“Mahaifina ya cika gwani, ya kwashe kimanin shekaru 40 yana aiki da NHS yana ceton rayuwar jama’a a nan da kuma Afirka, har zuwa lokacin da ya fara rashin lafiya, yana taimakawa wajen ceton rayukan jama’a.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel