Covid-19: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi

Covid-19: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da fitar da tan 70,000 daga ma'adanar hatsi ta kasa don raba wa mabukata a kasar nan a matsayin hanyar saukaka barnar da cutar coronavirus.

Sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban kwamitin shugaban kasa a kan COVID-19, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a Abuja yayin jawabi karo na uku na PTF a ranar Laraba.

Kamar yadda yace, tan 60,000 sau dubu na hatsi za a raba ne a jama'ar jihohi birnin tarayya, Legas da jihar Ogun. Sauran tan 10,000 sau dubu din kuwa za a raba ne ga mabukatan da ke sauran jihohin Najeriya.

Covid-19: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi
Covid-19: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Ya ce, "Mun samu rahoto daga hukumar kiyaye hadurra ta kasa a kan yadda zirga-zirga ke kasancewa a fadin kasar nan har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2020. Bayanai sun nuna cewa jama'a na bin doka da ka'idojin fadar shugaban kasan wanda hakan ya kawo ragowa a cunkoson manyan hanyoyi."

"Amma kuma mun samu rahotanni a kan kalubalen da wannan dokokin ke kawowa daga jami'an tsaro. Akwai kuma rahotanni daga jihohin da gwamnonin su suka saka dokar ta-baci," A cewar Mustapha.

Ya kara da cewa PTF ta habaka dokokin da sabbin tsare-tsare yayin rufe jihohin nan, wadanda za su zagaye kasar nan ta hannun cibiyoyin tsaro.

Idan zamu tuna, a ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe jihohin Lagos da Ogun tare da babban birnin tarayya. Hakan ta faru ne kuwa don hana yaduwar muguwar cutar coronavirus a kasar nan. Ya bada wannan umarnin ne a jawabin da yayi ga 'yan kasa a talabijin da gidajen rediyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel