Da duminsa: Mun amince a bude kasuwanni daga karfe 10 zuwa 2 a Legas, Abuja da Ogun - FG

Da duminsa: Mun amince a bude kasuwanni daga karfe 10 zuwa 2 a Legas, Abuja da Ogun - FG

- Gwamnatin tarayya ta ji kukan al'umma kan dokar hana fitar da ta sanya a jihohi uku

- Mutane zasu iya fita kasuwancinsu daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana a Legas, Abuja, da Ogun

- Wannan ya shafi kantuna da masu kayan abinci

Domin saukake dokar ta bacin da aka sanyawa mazauna jihar Legas, Ogun da birnin taraya Abuja, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa dukkan kasuwanni zasu iya budewa daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana kullum.

Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan yakar cutar COVID-19, Aliyu Sani, ya bayyana hakan.

Yace: "Ga yan kasuwa, shagunan sayar da kayan abinci da kayan masarufi kada aka amince su bude daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana."

"A tabbatar da cewa an gwada zafin jikin dukkan ma'aikatan kasuwa kuma duk wanda aka samu zafin jikinsa ya zarce 38 a ma'aunin Celcius, kada a bari ya shiga."

KU KARANTA: Buhari ya amince da fitar da hatsi tan 70,000 don raba wa al'umma marasa karfi

Da duminsa: Mun amince a bude kasuwanni daga karfe 10 zuwa 2 a Legas, Abuja da Ogun - FG
Kasuwa
Asali: Getty Images

A bangare guda, Wani direban motan haya da ya kamu da cutar Coronavirus ya gudu daga inda aka killaceshi a garin Bida, jihar Neja kuma na bazama nemansa yanzu.

Kwamishanan kiwon lafiyan jihar, Dakta Mohammed Makunsidi, ya alanta nemansa ruwa a jallo kuma gwamnati ta nada kwamiti na musamman domin nemoshi.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai jiya a Minna, Makunsidi yace: "Mun yi mamakin guduwarsa kuma yadda ya gudu daga asibitin abin mamaki ne garemu har yanzu amma an harzuka wajen kamoshi."

"Mun samu labarin cewa ya gudu cikin Bida, kuma muna biye da shi yanzu. Mambobin hukumar yaki da COVID-19 da jami'an ma'aikatar lafiya na Bida yanzu domin nemansa da kuma tabbatar da cewa ya yi abinda cibiyar NCDC ta umurcesa."

Kwamishanan ya kara da cewa an killace wasu mutane biyu da suka dawo daga kasar Birtaniya da Canada a garin Kontagora kuma ana gwada su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel