Kasashen da muke kallo a matsayin wadanda za su taimaka mana suma neman taimakon suke yanzu - Gwamnatin tarayya

Kasashen da muke kallo a matsayin wadanda za su taimaka mana suma neman taimakon suke yanzu - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta a kan yadda annobar coronavirus ke ci gaba da yaduwa a kasar nan

- Kamar yadda ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana, kasashen da gwamnatin tarayyar ke kallo don taimakawa suna kuka da annobar suma

- Kamar yadda ya ce, duk da hakan akwai kasashen da suka yi alkawarin dawo da 'yan Najeriya kasarsu kyauta tare da taimakawa da na'urorin taimakon numfashi

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa kasashen da take kallo da burin su tallafa mata wajen yaki da cutar coronavirus su ma na fuskantar annobar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Abuja a ranar Talata, Geoffrey Onyeama, ministan harkokin waje, ya ce kasashen har ila yau suna bada hadin kai.

Kasashen da muke kallo a matsayin wadanda za su taimaka mana suma neman taimakon suke yanzu - Gwamnatin tarayya

Kasashen da muke kallo a matsayin wadanda za su taimaka mana suma neman taimakon suke yanzu - Gwamnatin tarayya
Source: Depositphotos

Ya ce Najeriya na koyon hanyoyin da za ta yaki cutar coronavirus kuma tana samun bayanai daga wadanda ya kamata su taimaka mata da kayan gwajin cutar.

"Muna samun bayanai daga kasashen kuma muna koyo daga garesu. Muna kuma samun kayan aikin da bamu dasu daga wajensu," Onyeama yace.

"Kamar yadda kuka sani, bamu da na'urar taimakon numfashi isassu. A don haka ne muka saka kasashen cikin lamarin kuma muna fatan samu daga wajensu.

KU KARANTA: Kishi kumallon mata: Matar aure ta kashe kanta akan mijinta yayi mata kishiya

"Amma kuma kasashe masu yawa da muke kallonsu don taimako suna fuskantar barkewar cutar."

Ministan ya kara da cewa wasu daga cikin kasashen da suka shawo kan annobar na kokarin bada likitocinsu don shawo kan annobar wanda hakan zai matukar taimako.

"Wasu kasashen kuma na kokarin dawo mana da 'yan kasashenmu kyauta zuwa gida Najeriya. Hakazalika, za su taimaka wajen yakar annobar," yace.

Da karfe 8 na yammacin ranar Talata, Najeriya na da mutane 139 da suka kamu da cutar Coronavirus. Mutane biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon muguwar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel