LASU ta samar da manhajar gwajin cutar coronavirus ta wayoyi

LASU ta samar da manhajar gwajin cutar coronavirus ta wayoyi

- Sashen nazarin na'ura mai kwakwalwa na jami'ar jihar Legas (LASU) ta kirkiri manhaja mai iya gwada cutar coronavirus a jikin dan Adam

- Kamar yadda sashen ya bayyana, manhajar ta hadu ne sakamakon aikin da kungiyar malaman sashen da na kwalejin kiwon lafiya

- Kamar yadda kakakin jami'ar ya bayyana, manhajar za a iya samunta ne daga ranar 7 ga watan Afirilun 2020

Sashen nazarin na'ura mai kwakwalwa na jami'ar jihar Legas (LASU) ya samar da wata manhaja da za ta ba jama'a damar yin gwajin muguwar cutar coronavirus da kansu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban cibiyar yada labarai da hulda da jama'a na jami'ar, Ademola Adekoya, a takardar da ya fitar a ranar Talata, ya ce wannan kirkirar ta samu jagorancin Farfesa Benjamin Aribisala tare da sauran 'yan kungiyar.

LASU ta samar da manhajar gwajin cutar coronavirus ta wayoyi

LASU ta samar da manhajar gwajin cutar coronavirus ta wayoyi
Source: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus ta kashe mutum fiye da 40,000 a fadin duniya

Sauran 'yan kungiyar sun hada da Dr. Oluwatoyin Enikuomehin, Olusola Olabajo, Abdulazeez Saheed da kuma Dr. Abdulazeez Anjorin.

Kamar yadda ya sanar, manhajar za ta iya samuwa ne a Google PlayStore daga ranar Talata, 7 ga wata Afirilun 2020.

Ya kara da bayyana cewa an gwada manhajar kuma an tabbatar da tana amfanin da aka gina ta a kai. Shugaban kwalejin kiwon lafiya na jami'ar da ke Ikeja ya aminta da manhajar.

A wani rahoton, kun ji cewa kwamishinan Lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya yi karin bayani a kan lafiyar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba Kyari da aka gano yana dauke da coronavirus a makon da ta gabata.

Abayomi ya bayyana cewa bai san inda Abba Kyari ya ke ba a halin yanzu amma ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar yana lafiya kuma yana cikin farin ciki a lokacin da suka yi hira ta manhajjar Whatsapp kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Kwamishinan yayin amsa tambayoyin manema labarai a ranar Talata 31 ga watan Maris ya ce; "Ban tsan tsarin tafiye-tafiyen shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar ba saboda haka ban san inda ya ke ba a yanzu.

Mun gaisa amma ta Whatsapp amma kuma ba za ka iya sanin inda mutum ya ke ba ta whatsapp.

"Muna magana lokaci zuwa lokaci amma ban tambayi inda ya ke ba. Bisa alamu yana cikin koshin lafiya da farin ciki kuma muna tattaunawa ne a kan batuttuwan da suka shafi tsare-tsare saboda haka ya dade da muka yi magana game da lafiyarsa saboda haka ina tsamanin ya warke."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel