Annobar Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana shige da fice

Annobar Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana shige da fice

Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da sarara dokar takaita zirga zirga da kuma na hana shige da fice a duk fadin jahar daga ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu na shekarar 2020.

Kwamishinan al’amuran cikin gida da tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda yace gwamnatin ta dage dokar ne domin baiwa jama’an jahar dama fita su sayo kayan abinci, kayan masarufi da sauran kayan bukatun yau da kullum.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu

Sai dai dokar dagewar ta zo da wani sabon salo, ba kamar yadda aka saba gani ba a duk lokacin da gwamnati ta sanya kwatankwacin irin wannan doka, ga dai yadda kwamishina Aruwan ya bayyana ta.

“Gwmanatin jahar Kaduna ta sanar da dage dokar hana zirga zirga na wucin gadi daga karfe 3 na rana zuwa karfe 12 na dare, har zuwa gobe Alhami, 2 ga watan Afriulu. An yi haka ne don baiwa jama’a daman tara abinci da sauran bukatun yau da kullum.

“Amma daga gobe, za’a cigaba da dokar hana zirga zirga, illa a ranakun Talata da Laraba ne kadai za’a dinga sarara dokar.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Wasu gungun miyagun yan bindiga sun halaka mutane 11 a jahar Kaduna duk da dokar hana shige da fice da zirga zirga da gwamnatin jahar ta sanya, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Mai magana da yawun kungiyar mutanen kudancin Kaduna, SOKAPU, Luka Binniyat ne ya bayyana haka inda yace an kai harin ne a mazabar Guruku dake kauyen Kuduru cikin karamar hukumar Chikun da Jagindi na karamar hukumar Jama’a.

A cewar Binniyat, dakacin Jagindi, Danlami Barde tare da kaninsa Musa na daga cikin mutanen da yan bindigan suka kashe a yayin harin da suka kai a ranar Litinin, 30 ga watan Maris. Haka zalika maharan sun kashe mutane 6 a Guruku.

Binniyat ya cigaba da cewa ko a ranar Alhamis sai da aka kashe mutane uku a Kuduru, sa’annan yan bindigan suka banka ma gidajensu wuta bayan sun sace duk wani mai muhimmanci a gidajen, daga cikin wadanda suka kashe akwai Halima Bala, Jamilu Hassan da Hassana Bala.

Kungiyar SOKAPU ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bincike game da harin, sa’annan ta kai ma mutanen da harin ya shafa dauki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel