Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta samar da kayan tallafi na N500m ga 'yan jihar marasa galihu

Coronavirus: Gwamnatin Kaduna ta samar da kayan tallafi na N500m ga 'yan jihar marasa galihu

- Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kayan abincin na Naira miliyan 500 don tallafi ga mabukata

- Kwamishinar walwala da jin dadi a jihar, Hajiya Hafsat Baba ta tabbatar da cewa rabon zai zagaya kananan hukumomi 23 na jihar

- Kamar yadda ta ce, limamai, mataimakansu, fastoci da dattijan mata biyu a kowanne yanki ne za su jagoranci rabon

Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kayayyakin abinci na naira miliyan 500 don rabawa ga masu tsananin bukata a jihar. Kamar yadda gwamnatin ta bayyana, hakan zai zama tallafi da tausayawa ga talakawa sakamakon bayan dokar ta-bacin da aka saka don hana yaduwar cutar coronavirus.

Kwamishinan walwala da jin kai ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta sanar da hakan a yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a ranar Laraba a garin Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Dokar ta-baci: Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kayan tallafi na N500m ga 'yan jihar

Dokar ta-baci: Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kayan tallafi na N500m ga 'yan jihar
Source: Original

DUBA WANNAN: Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Baba ta ce an fara rabon kayayyakin ne a karamar hukumar Sabongari ta jihar. Kwamishinar ta kara da cewa, jihar tana bayar da wannan tallafin ne don ta hannu kwamitin tallafi na jihar ta yadda za su kai duk inda ake bukata.

Kamar yadda tace, kayayyakin za a bada su ne a kungiyance wanda za a raba su ga mabukatan.

Ta ce an zabi kungiyoyin ne daga kananan hukumomi 23 na jihar. "Wadanda za su dau nauyin rabon sun hada da Limami, mataimakansu, fastoci, shugabannin yankuna da kuma dattijan mata biyu a kowanne yanki," in ji ta

Kwamishinar ta kara da cewa, jami'an gwamnati ne za su jagoranci rabon a dukkan kananan hukumomin jihar.

A wani labarin, kun ji cewa wasu gungun miyagun yan bindiga sun halaka mutane 11 a jahar Kaduna duk da dokar hana shige da fice da zirga zirga da gwamnatin jahar ta sanya, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun kungiyar mutanen kudancin Kaduna, SOKAPU, Luka Binniyat ne ya bayyana haka inda yace an kai harin ne a mazabar Guruku dake kauyen Kuduru cikin karamar hukumar Chikun da Jagindi na karamar hukumar Jama’a.

A cewar Binniyat, dakacin Jagindi, Danlami Barde tare da kaninsa Musa na daga cikin mutanen da yan bindigan suka kashe a yayin harin da suka kai a ranar Litinin, 30 ga watan Maris. Haka zalika maharan sun kashe mutane 6 a Guruku.

Binniyat ya cigaba da cewa ko a ranar Alhamis sai da aka kashe mutane uku a Kuduru, sa’annan yan bindigan suka banka ma gidajensu wuta bayan sun sace duk wani mai muhimmanci a gidajen, daga cikin wadanda suka kashe akwai Halima Bala, Jamilu Hassan da Hassana Bala.

Kungiyar SOKAPU ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bincike game da harin, sa’annan ta kai ma mutanen da harin ya shafa dauki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel