Dokar zama a gida: Zamu samar muku da isasshen wutan lantarki - GenCos sunyi alkawari

Dokar zama a gida: Zamu samar muku da isasshen wutan lantarki - GenCos sunyi alkawari

Kamfanonin samar da wutan lantarkin Najeriya GenCos, sun yi alkawarin tabbatar da cewa ana cigaba da samun isasshen wuta a kasar wannan lokacin na zama a gida.

Sakatariyar kungiyar kamfanonin, Joy Ogaji, ta bayyana hakan ne ranar Laraba a birnin tarayya, Abuja.

Gaji ta ce GenCos na hada kai da juna wajen tabbatar da cewa yan Najeriya sun samu isasshen wutan lantarki yayin annobar Coronavirus.

Tace"Mun kara yawan wutan da muke samarwa zuwa Migawat 4,024 tun lokacin da aka samu bullar cutar ranar 27 ga Febrairu."

"Yayinda muke cigaba da ganin ana cigaba da aiki, GenCos na iyakan kokarin tabbatar da cewa aiki na tafiya saboda kada hakan ya shafi tattalin arziki."

Dokar zama a gida: Zamu samar muku da isasshen wutan lantarki - GenCos sunyi alkawari

Dokar zama a gida
Source: UGC

KU KARANTA: Najeriya ta na cikin karancin na’ura a tsakiyar annobar COVID-19

Hukumar daidaita farashin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce ta dakatar da karin kudin wutar lantarki wanda ta tsara zai fara aiki a ranar 1 ga watan Afirilu.

Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Talata bayan da hukumar ta wallafa hakan a shafinta na twitter. Ta ce, "Ba za a kara farashin wutar lantarki ba kamar yadda hukumar ta sanar a ranar 1 ga watan Afirilu, 2020."

Mai magana da yawun NERC, Usman Arabi, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times cewa hukumar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter.

Da safiyar yau Talata ne kungiyar kwadago ta kushe karin farashin wutar lantarkin.

Shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, a wata takardar da ya fitar, ya ce wannan karin farashin ba wani abu zai kara ba da ya wuce karin matsi ga 'yan Najeriya bayan takurar da annobar coronavirus ta yi musu.

A watan Disamban 2019 ne NERC ta bayyana cewa za ta kara farashin wutar lantarki a ranar 1 ga watan Afirilun 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel