Coronavirus: Yawan majinyatan da suka mutu a Amurka sun zarce na China

Coronavirus: Yawan majinyatan da suka mutu a Amurka sun zarce na China

Kasar Amurka ta sha gaban kasar China a yawan jama'ar da suka rasa rayukansu sakamakon annobar cutar coronavirus.

Kamar yadda www.worldometers.info ta bayyana a ranar Laraba, rayuka 3,850 ne suka salwanta sakamakon barkewar cutar a Amurka. Wannan kuwa ya zarta na kasar China masu mutuwar mutane 3,305.

Muguwar cutar numfashin dai ta fara ne daga Wuhan a kasar China kuma ta fada sassa da dama na duniya inda ta lamushe rayuka daban-daban.

Amurka wacce a halin yanzu ke kan gaba wajen yawan masu cutar a duniya, ta zamo daya daga cikin kasashe uku na duniya da cutar ta yi wa babbar barna.

A yayin da kasar Italiya ke da mutane 12,428 masu cutar, kasar Spain ta rasa rayuka 700 a ranar Talata.

Adadin mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka ya dara wadanda suka mutu a China

Adadin mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka ya dara wadanda suka mutu a China
Source: Instagram

DUBA WANNAN: Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Birnin New York ne cutar ta fi barkewa a kasar Amurka.

Kamar yadda kwararru suka bayyana, akwai yuwuwar mace-macen su ninka saboda wasu na mutuwa ne ba tare da anyi musu gwajin cutar ba.

Kasashen duniya na ci gaba da bayyana rashin kayan gwajin cutar wanda ya zamo babban kalubale gare su. Cutar kuwa ta zama gagararriya ga masana kimiyya har a halin yanzu.

A halin yanzu, nahiyar Afirka ce ke da kaso mafi karanci na mutuwa sakamakon cutar a nahiyoyin duniya.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta bayyana, babu wata kasa a nahiyar Afrika da ta samu mutuwar mutum 50. Egypt ce ke da mutane mafi yawa da suka mutu sakamakon cutar inda kasashen Algeria da Morocco ke biye.

Kasar Afrika ta Kudu ce ke da mutane 1,000 da suka kamu da cutar amma mutane 3 kacal suka rasa.

A cikin mutane 161 da ke da cutar a kasar Ghnay, 31 sun warke wanda shine mafi yawa a nahiyar Afrika.

Najeriya na da mutane 139 da suka kamu da cutar a ranar Talata da yamma sannan ta rasa rayuka biyu. Mutane 8 ne suka warke bayan kamuwa da cutar kuma aka sallame su daga asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel