Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu

Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, mun samu labarun rasuwar Alhaji Sa’ada Usman, Sarkin Jere na karamar hukumar Kagarko ta jahar Kaduna.

Sarkin ya rasu ne bayan doguwar jinya da yayi fama da shi. Alhaji Sa’ad Usman shi ne mijin tsohuwar ministar kudi, kuma tsohuwar Sanatan Kaduna ta kudu, Sanata Nenadi Usman.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnati za ta yi ma yan Najeriya 1,500 gwaji a duk rana

Wakilin watsa labaru na Jere, Ahmad D Yako ne ya bayyana haka a shafinsa na dandanin sadarwar zamani na Facebook, inda yace za’a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a fadar masarautar Jere.

Da fatan Allah Ya jikan shi da gafara.

Da dumi dumi: Babban basaraken jahar Kaduna ya rasu

Sarkin Jere
Source: Facebook

Idan za'a tuna a shekarar 2014 ne wasu mutane suka kai ma Sarkin hari yayin da ya je yin sulhu tsakanin wasu bangarori biyu da basa ga maciji da juna a lokacin da wata rikici a kan fili ta taso a tsakaninsu.

A dalilin wannan hari, Sarkin ya samu munanan rauni a kansa, wanda hakan tasa aka garzaua da shi wani babban asibiti Cedar dake babban birnin tarayya Abuja a, daga bisani kuma aka mika shi zuwa asibitin kasar waje.

Sai dai daga bisani rundunar Yansandan jahar Kaduna ta tabbatar da kama wasu daga cikin mutanen da suka kai ma Sarkin hari, kamar yadda kaakakin rundunar na wancan lokaci, Aminu Lawan ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel