Yan bindiga sun kashe mutane 11 a jahar Kaduna duk da dokar hana zirga zirga

Yan bindiga sun kashe mutane 11 a jahar Kaduna duk da dokar hana zirga zirga

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun halaka mutane 11 a jahar Kaduna duk da dokar hana shige da fice da zirga zirga da gwamnatin jahar ta sanya, kamar yadda jaridar The Cables ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun kungiyar mutanen kudancin Kaduna, SOKAPU, Luka Binniyat ne ya bayyana haka inda yace an kai harin ne a mazabar Guruku dake kauyen Kuduru cikin karamar hukumar Chikun da Jagindi na karamar hukumar Jama’a.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnati za ta yi ma yan Najeriya 1,500 gwaji a duk rana

A cewar Binniyat, dakacin Jagindi, Danlami Barde tare da kaninsa Musa na daga cikin mutanen da yan bindigan suka kashe a yayin harin da suka kai a ranar Litinin, 30 ga watan Maris. Haka zalika maharan sun kashe mutane 6 a Guruku.

Binniyat ya cigaba da cewa ko a ranar Alhamis sai da aka kashe mutane uku a Kuduru, sa’annan yan bindigan suka banka ma gidajensu wuta bayan sun sace duk wani mai muhimmanci a gidajen, daga cikin wadanda suka kashe akwai Halima Bala, Jamilu Hassan da Hassana Bala.

Kungiyar SOKAPU ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gudanar da cikakken bincike game da harin, sa’annan ta kai ma mutanen da harin ya shafa dauki.

Sai da majiyarmu ta tuntubi rundunar Yansandan jahar don jin ta bakinta game da harin, sai kaakakin rundunar, Muhammadu Jalige ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da hare haren, amma zai bincika.

A wani labarin kuma, dakarun rundunar Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun ragargaza wani sansanin mayakan kugiyar ta’addanci ta Boko Haram a yankin Ngoske na dajin Sambisa dake jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya labarun Najeriya ta ruwaito daraktan watsa labaru na shelkwatar tsaro ta Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

Onyeuko yace rundunar ta samu wannan nasara ne sakamakon wani samame ta sama da dakarun sashin rundunar Sojan sama na Operation Lafiya Dole suka kai ma yan ta’addan mai taken Operation Decisive Edge a ranar Litinin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel