Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota

A kalla mutane 30 ne suka samu raunika bayan wani tsoho mai shekaru 50 ya daka tsalle daga motar haya a kasuwar Otu Ocha da ke karamar hukumar Aguleri ta jihar Anambra. Hakan kuwa ya faru ne bayan daya daga cikin fasinjojin motar ya yi tari.

Kamar yadda ganau ba jiyau ba suka sabar, tsoratattun fasinjojin sun yi zaton fasinja na da cutar coronavirus.

Mutane sun tabbatar da cewa kwandastan ne ya fara gudu inda sauran fasinjoji suka rufa mishi baya. Wannan kuwa ya kawo hargitsi a yankin don mutane 30 ne suka samu rauni.

Amma kuma rahotannin da ba a tabbatar ba kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito, sun ce a kalla mutane 30 ne suka samu miyagun raunika.

Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota
Coronavirus: Yadda fasinjoji suka 'tarwatse' bayan wani ya yi atishawa cikin mota
Asali: Twitter

Kwandastan da ya fara dirowa daga motar bai san komai a kan cutar ba kamar yadda ya bayyana. Ya ce a tunanin shi duk wanda yake tari yana dauke da cutar ne kuma kamata yayi a damke shi a mika cibiyar killacewa.

DUBA WANNAN: Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Bayan gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano yayi kira ga jama'ar jihar, 'yan sandan sun dinga wayar da kan jama'a a kan cutar.

Wannan wayar da kan kuwa ya samu jagorancin DPO din babban ofishin 'yan sandan, SP Ifeanyi Iburru tare da manyan jami'an 'yan sandan jihar.

A makon da ya gabata ne Obiano ya bada umarnin rufe dukkan makarantun jihar. Gwamnan ya kara da haramta duk taron da jama'a 30 za su hadu wuri daya. Wadannan tarukan kuwa sun hada da bukukuwan aure, birne mamaci, bikin shigowar sabuwar doya, taron siyasa da wuraren bauta.

Gwamnan ya kara da umartar dukkan masu adaidaita sahu a jihar da su debi fasinjoji biyu take inda masu motocin haya za su diba uku.

Ya kara da umartar jami'an tsaro na jihar da su tabbatar da cewa jama'a sun yi biyayya ga sabbin tsarikan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel