Deji Adeleke ya bada kyautar Biliyan 1 a lokacin annobar cutar COVID-19

Deji Adeleke ya bada kyautar Biliyan 1 a lokacin annobar cutar COVID-19

Mista Deji Adeleke ya shiga jerin Attajiran da su ka taimaka da dukiyarsu wajen bada tallafi a yayin da mutanen Najeriya su ke fama da annobar cutar nan ta COVID-19.

Deji Adeleke wanda hamshakin ‘Dan kasuwa ne, ya bada gudumuwarsa da nufin taimakawa wajen yakar cutar Coronavirus da yanzu ta kashe mutane biyu a Najeriya.

Adeleke ya bada gudumuwar Naira biliyan daya domin agazawa ‘Yan Najeriya. Attajirin ya raba wannan gudumuwa ne ta bada kyautar tarin kudi da kuma kayan abinci.

Fitaccen ‘Dan jaridar nan Dele Momodu, shi ne ya bayyana mana wannan a Ranar Talata. ‘Dan kasuwar ya ba gwamnatin tarayya gudumuwar kudi Naira miliyan 500.

Bayan haka, Deji Adeleke ya raba kayan abinci ga mutanen jiharsa. Adeleke ya rabawa mutanen jihar Osun abinci na makamancin wannan kudi har Naira miliyan 500.

KU KARANTA: 'Yan Majalisa sun bada tallafin miliyoyi domin kawo karshen Coronavirus

Dele Momodu da ya ke bayyana wannan a shafinsa na Tuwita a jiya, 31 ga Watan Maris, 2020, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji ya kara wadata aljihun wannan Bawan Allah.

Ga wadanda ba su da labari, Deji Adeleke mai shekaru 63 a Duniya shi ne Mahaifin Tauraron Mawakin nan watau Davido wanda ya yi tashe a Najeriya da ma Afrika.

Attajirin shi ne Mai jami’ar nan ta Adeleke University a Kudancin Najeriya. Haka zalika shi ne shugaban babban kamfanin Pacific Holdings da ke zaune a Garin Legas.

Idan ba ku manta ba irinsu Abdussamad Rabiu, Aliko Dangote, Mike Adenuga, Folorunsho Alakija duk sun bada gudumuwarsu domin ganin bayan COVID-19 a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel