Coronavirus ta kashe mutum fiye da 40,000 a fadin duniya

Coronavirus ta kashe mutum fiye da 40,000 a fadin duniya

Bayan kasashen Spain da na Amurka sun kasance wadanda suka fi yawan mace-mace sakamakon annobar coronavirus a ranar Talata, jimillar wadanda suka mutu sakamakon cutar sun kai mutane 40,000.

A yayin daukar rahoton, worldometers.info ta gano cewa mutane 40,000 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar.

Kwararru sun yarda cewa za a iya samun ninkin mutuwar nan ba tare da anyi wa masu cutar gwajin ba.

Kasashe da dama sun ci gaba da korafin rashin kayan gwajin cutar, wacce har yanzu ta gagari kimiyya.

Wannan yawan mutuwar sakamakon cutar ta zo ne bayan da cutar ta kama mutane 800,000 a fadin duniya, wanda masu hasashe suka tabbatar da cewa nan da kwanaki kadan za a kai mutane miliyan daya.

Covid-19: Dalla-dallar yawan jama'ar da suka rasa rayukansu a kasashen duniya

Covid-19: Dalla-dallar yawan jama'ar da suka rasa rayukansu a kasashen duniya
Source: UGC

DUBA WANNAN: Coronavirus: Gwamnatin tarayya za ta bawa 'yan Najeriya miliyan 11 tallafi

Turai ce ta zamo yankin da cutar ta fi kamari don jimillar wadanda suka rasu a kasar Italiya da Spain sun kai 20,000.

A kasar Amurka ne kwayar cutar ta fi kama mafi yawan jama'a a duniya don kuwa mutane 160,000 ne suka kamu da cutar a kasar.

Akwai yuwuwar yawan wadanda za su mutu masu cutar a Amurka su shafe na kasar China, duk da kuwa cutar ta samo asali ne daga kasar nahiyar Asia din a watan Disamban da ta gabata.

Spain ta zama kasa ta hudu a duniya da cutar ta fi yi wa illa inda aka samu mutuwar mutane 800 a cikin sa'o'i 24.

Kasar Faransa ta samu mutane a kalla 3,000 da suka kamu da cutar inda mutane 1,400 suka rasa rayukansu a Ingila.

Yawan mace-mace sakamakon annobar kuwa a Afrika har yanzu babu yawa idan aka danganta da sauran sassan duniya.

Babu kasar da aka samu mutane 50 har yanzu da suka rasa rayukansu sakamakon cutar a Afrika. Kasar Egypt ce a kan gaba wacce ta rasa mutane 41, Algeria ta rasa mutane 35 sai kasar Morocco wacce ta rasa mutane 33 sakamakon barkewar annobar.

Kasar Afrika ta Kudu ce ke kan gaba a nahiyar Afrika inda take da mutane 1,000 masu cutar amma mutane uku kacal suka mutu.

A ranar Talata ne Najeriya ke da mutane 135 masu cutar da kuma mutuwar mutane biyu. A kalla mutane takwas ne suka warke daga cutar kuma aka sallamesu daga asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel