Sojoji sun sake kassara kungiyar Boko Haram a wani samame da suka kai musu ta sama

Sojoji sun sake kassara kungiyar Boko Haram a wani samame da suka kai musu ta sama

Dakarun rundunar Sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole sun ragargaza wani sansanin mayakan kugiyar ta’addanci ta Boko Haram a yankin Ngoske na dajin Sambisa dake jahar Borno.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya labarun Najeriya ta ruwaito daraktan watsa labaru na shelkwatar tsaro ta Najeriya, Birgediya Benard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata.

KU KARANTA: Duniya ta yi dadi: Kansila ya aure mata 2 a rana daya a jahar Nassarawa

Onyeuko yace rundunar ta samu wannan nasara ne sakamakon wani samame ta sama da dakarun sashin rundunar Sojan sama na Operation Lafiya Dole suka kai ma yan ta’addan mai taken Operation Decisive Edge a ranar Litinin.

“Biyo bayan samun sahihan bayanan sirri da suka tabbatar da taruwar yan ta’adda a wani sansaninsu dake cikin dajin Sambisa, hakan ne tasa aka tura jiragen yakin Najeriya zuwa yankin suka musu luguden wuta.

“Jiragen yakin sun samu nasarar lalata sansanin gaba daya tare da kashe gomman mayakan Boko Haram. Hukumomin tsaron Najeriya za su cigaba da dagewa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Arewa maso gabas, ta hanyar cigaba da ragagazan makiyan Najeriya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, zaratan dakarun rundunar Sojin Najeriya dake aikin Operation Lafiya Dole sun samu nasarar halaka wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Abu Usamah tare da gomman mayakan ta’addanci.

Shugaban sashin watsa labaru na rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, inda yace Sojojin sun samu wannan nasara ne a karan battan da suka yi da Boko Haram a Gorgi, karamar hukumar Damboa.

A cewar Onyeuko, wannan nasara da rundunar Sojin Najeriya ta samu ya samar da wata babbar gibi a shugabancin kungiyar Boko Haram, ya kara cewa sun kwato bindigar AK-47 guda 2, albruusai, bindigar harba Bom da sauran ababe da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel