Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4; 3 a Abuja, 1 a Legas

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4; 3 a Abuja, 1 a Legas

Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane hudu da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.

Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Talata inda tace: “An tabbatar da mutane hudu sun kamu da #COVID19 a Najerya. 3 a Abuja, 1 a Legas, .“

“Dai-dai Karfe 8:00 na daren 31 ga Maris, mutane 139 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami tara, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“

Ga jerin jiha-jiha

Lagos- 82

Abuja - 28

Oyo- 8

Osun- 5

Ogun- 4

Kaduna- 3

Enugu- 2

Edo- 2

Bauchi- 2

Ekiti- 1

Rivers-1

Benue- 1

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4; 3 a Abuja, 1 a Legas
Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4; 3 a Abuja, 1 a Legas
Asali: Facebook

A bangare guda, Gwamnatin jihar Ekiti ta sanar da cewa an sallami mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus da mai kula da shi daga cibiyar killace masu cutar a jihar.

Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita ranar Talata inda tace mutumin ya tafi gida bayan kwashe kwanaki 12 a killace.

Hakazalika, Gwamnatin jihar Oyo ta alanta cewa mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar ya samu sauki kuma an sallamesa.

Wannan ya biyo bayan labarin tabbatar da kamuwar gwamnan jihar, Seyi Makinde, da cutar.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Taiwo Adisa, ya bayyana cewa “An sallami wanda ya fara kamuwa da cutar COVID-19 da aka killace.”

“An sallameshi ne bayan kammala jinyarsa a cibiyar killace mutane dake asibitin Agbami Chest dake Ibadan, babbar birnin jihar.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel