Gwamnatin jihar Kaduna ta mayar da almajirai 20,000 jihohinsu na asali
- A karo na biyu, gwamnatin Kaduna na fitittikan almajirai daga jihar
- Maimakon haramta bara a jihar, gwamnatin na mayar da yaran jihohinsu na asali
Gwamnatin jihar Kaduna ta kwashe yara almajirai 20,000 daga jihar zuwa jihohinsu na asali.
Kwamishanar harkokin mutane da jin dadin al’umma, Hafsat Baba, ta bayyana adadin yara da manyan Almajiran da aka mayar jihohi 16 tun makonni biyu da aka kaddamar da shirin.
Ta kara da cewa akwai yan kasar waje musamman daga Nijar cikin almajiran.
A cewarta: “Kawo yanzu, mun mayar da almajirai 20,736 yara da manya jihohinsu 17 da kuma wadanda suka zo daga kasar Nijar.”
“Amma har yanzu akwai wasu malaman da ke boye yaran daga hukuma musamman a wajen gari.”

Asali: UGC
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 4; 3 a Abuja, 1 a Legas
Shugaban kungiyar malaman Tsangaya, Sheikh Rabiu Abdullahi, ya yi kira ga Malaman makarantun tsangayar dake jihar su kulle makarantun saboda an kulle duka makarantun Boko da Islamiyya sakamakon cutar Coronavirus.
Yace: “Shi yasa muke kira ga mambobinmu su bi umurnin gwamnati ta hanyar mayar da yaran gidajensu na tsawon wannan lokaci. Muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan annobar.”
A baya, mun kawo muku rahoton cewa Wani almajiri ya halaka bayan ruwa ya tafi dashi a yayin da yake boyewa gwamnatin jihar Kaduna da ta bada umarnin kwashe almajirai daga jihar a matsayin hanyar hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.
An gano cewa malamin almajirin mai suna Malam Umar Musa Mai kalanzir ne ya boye shi a wajen bakin ruwa da ke Kabala West ta karamar hukumar Kaduna ta Kudu. A nan ne kuwa ya hadu da ajalin shi.
Bayan barkewar annobar Coronavirus ne gwamnatin jihar ta bayyana rufe duk makarantu wadanda suka hada da na tsangaya tare da umartar dukkan almajirai da su koma gaban iyayensu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng