Coronavirus: Gwamnatin tarayya za ta bawa 'yan Najeriya miliyan 11 tallafi

Coronavirus: Gwamnatin tarayya za ta bawa 'yan Najeriya miliyan 11 tallafi

Gwamnatin tarayya ta ce kyautatawar da za ta yi da yi wa 'yan Najeriya sakamakon halin da kasar nan ke ciki na barkewar cutar coronavirus za ta kai ga 'yan kasa miliyan 11.

Hakazalika, gwamnatin ta ce za ta kara kokari wajen samar da wuraren gwajin kwayar cutar ta Covid-19 da aka fi sani da coronavirus.

Ministar walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, a yayin jawabi a kan barkewar cutar a birnin tarayya Abuja, ta bayyana cewa 'yan gudun hijira da ka yankunan Arewa maso gabas din kasar nan tuni suka samu kayan tallafi na watanni biyu.

Coronavirus: Taimako daga FG zai isa ga 'yan Najeriya miliyan 11

Coronavirus: Taimako daga FG zai isa ga 'yan Najeriya miliyan 11
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

Ta ce tuni gwamnati ta samu rijistar wadanda basu da karfi a jihohi 35 na kasar nan wanda a kalla sun kai miliyan 2.6.

A yayin jawabi, darakta janar na hukumar kula da cutuka masu yaduwa, Dr Chike Ihekweazu ya ce Najeriya za ta ci gaba da halaka yawan gwajin cutar da za ta dinga yi a mako daya.

Za ta habaka har ta iya gwajin mutane 1,000 a sati daya. Tana fatan iya gwajin mutane 1,500 a sati me zuwa.

A wani labarin, kun ji cewa mazauna gidan gyaran hali a jihar Kaduna sun yi yunkurin balle gidan gyaran halin bayan rikici ya barke a kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

'Yan gidan gyaran halin, wadanda suka ji tsoron samun cutar sakamakon rashin isasshiyar iska mai tsafta da kuma kayan kariya daga cutar, sun taru da yawansu a safiyar yau Talata inda suka yi yunkurin ballewa su tsere daga gidan gyaran halin.

Jami'an tsaro da suka dinga harbi a farfajiyar gidan gyaran halin don tsorata 'yan gidan gyaran halin tare da saisata komai.

A halin yanzu mutum daya ne ake tsammanin ya rasa ransa sakamakon rikicin amma jami'ai masu yawa sun samu raunika inda aka gaggauta mika su asibiti don taimakon likitoci.

Wani jami'i a gidan, wanda yayi magana da bukatar a sakaya sunansa a ranar Talata, ya ce bangarori da yawa na gidan duk sun lalace sakamakon barnar mazauna gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel