Covid-19: An dakatar da karin kudin wutan lantarki da aka shirya yi a Najeriya
Hukumar daidaita farashin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta ce ta dakatar da karin kudin wutar lantarki wanda ta tsara zai fara aiki a ranar 1 ga watan Afirilu.
Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Talata bayan da hukumar ta wallafa hakan a shafinta na twitter. Ta ce, "Ba za a kara farashin wutar lantarki ba kamar yadda hukumar ta sanar a ranar 1 ga watan Afirilu, 2020."
Mai magana da yawun NERC, Usman Arabi, ya tabbatar wa da jaridar Premium Times cewa hukumar ce ta wallafa hakan a shafinta na Twitter.
Da safiyar yau Talata ne kungiyar kwadago ta kushe karin farashin wutar lantarkin.

Asali: Depositphotos
DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Mazauna gidan gyaran hali sun yi yunkurin ballewa su tsere a Kaduna
Shugaban kungiyar kwadago na kasa, Ayuba Wabba, a wata takardar da ya fitar, ya ce wannan karin farashin ba wani abu zai kara ba da ya wuce karin matsi ga 'yan Najeriya bayan takurar da annobar coronavirus ta yi musu.
A watan Disamban 2019 ne NERC ta bayyana cewa za ta kara farashin wutar lantarki a ranar 1 ga watan Afirilun 2020.
Da yawan jihohin Najeriya duk an hana walwala tare da rufesu sakamakon annobar coronavirus da duniya ke fama da ita.
An rufe dukkan makarantun Najeriya yayin da gwamnatocin jihohi suka hana yawo a cikin jihohi.
A halin yanzu dai Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutane 135 na kasar da muguwar cutar coronavirus.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng