Za mu kama gwamnati Idan Zakzaky ya mutu saboda Coronavirus – Yan Shia

Za mu kama gwamnati Idan Zakzaky ya mutu saboda Coronavirus – Yan Shia

Biyo bayan samun rahotanni dake nuna cewa an samu bullar annobar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a kurkukun jahar Kaduna, kingiyar yan Shia ta Najeriya, IMN, ta koka kan halin da shugabanta, Ibrahim Zakzaky ya shiga.

Daily Nigerian ta ruwaito IMN ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunta, Ibrahim Musa wanda yace gwamnatin tarayya za su kama idan wani abu ya samu shugabansu a kurkukun Kaduna.

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya garkame Borno, yace Coronavirus ta fi karfin Boko Haram

A cewarsa, aikin gwamnatin tarayya ne ta kare dukkanin mazauna gidan yari, musamman bayan samun bullar cutar Coronavirus a gidan yarin Kaduna, saboda aiki doka cewa ta yi wanda ake zargi ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar masa da laifin.

“Rahotanni sun bayyana cewa an samu rikici a gidan yarin Kaduna inda gwamnati ke cigaba da rike shugabanmu Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa bisa haramci, wanda hakan tasa har aka bude wuta tare da rufe hanyoyin da suka bi wurin.

“Mun damu kwarai da gaske sakamakon aukuwar wannan rikici, don haka muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da lafiyar Sheikh da matarsa, saboda dama kotun tarayya ta bayyana haramcin cigaba da rike shi a saboda an keta hakkinsa da yancin.

“Haka zalika wasu kotuna guda biyu sun yi fatali da tuhume tuhumen da ake masa bayan sun sallami ire iren tuhume tuhumen da aka shigar da kusan yan Shia 200 a kansu a gabansu.” Inji shi.

Daga karshe kungiyar IMN ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin Zakzaky tare da matarsa.

A wani labarin kuma, a kokarinta na rangwanta ma al’ummar Najeriya bisa mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon barkewar annaobar Coronavirus, gwamnatin Najeriya ta nemi kamfanonin sadarwa su sassauta ma yan Najeriya.

Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Ministan sadarwa, Sheikh Dakta Isah Ali Pantami, wanda ya bayyana haka a shafinsa na dandalin sadarwar zamani ta Facebook a daren Talata, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel