Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya

Sakamakon gwajin kwayar cutar Covid-19 da aka yi wa Sufeta Janar (IGP) na Rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya nuna cewa ba ya dauke da kwayar cutar.

IGP din ya samu sakamakon gwajinsa da safiyar yau 31 ga watan Maris bayan an dauki jininsa domin gwajin a ranar Juma'a 27 ga watan Maris na 2020 kamar yadda Kakakin rundunar, Frank Mba ya bayyana cikin sanarwar da ya fitar.

Mba shima ya bayyana cewa ya yi gwajin kuma sakamakon ya nuna baya dauke da kwayar cutar kamar yadda Daily Trust ta ruwait

Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya
Coronavirus: An fitar da sakamakon gwajin Shugaban 'Yan sandan Najeriya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

Ya kuma ce wasu daga cikin jami'an rundunar da suka yi gwajin kuma ba su kamu da cutar ba sun hada da; Shugaban ma'aikatan IGP, DCP Idowu Owohunwa; Shugaban sashin bayyanai sirrin, DCP Lanre Ogunlowo; Likitan IGP, CSP (Dakta) Nonye Welle; Jami'in Lafiya na Asibitin Hedkwatan 'Yan sanda na Abuja CSP (Dakta) Titus Adegbite; Sakataren IGP, SP Moses Jolugbo da wasu jami'an yan sanda 5 da ke kusa da IGP.

Sanarwa ta shawarci jami'an rundunar a dukkan jihohin Najeriya su cigaba da kulawa da dokokin da masana kiwon lafiya suka bayar na kare kansu da kamuwa daga cutar duk da cewa aikin dan sanda yana bukatar hulda da al'umma.

Ya kuma shawarci al'ummar kasa su yi biyaya ga shawarwarin kwararru da fanin kiwon lafiya da likitoci da jami'an tsaro domin kare kansu daga kamuwa daga muguwar cutar mai kisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel