Yanzu-yanzu: Mazauna gidan gyaran hali sun yi yunkurin ballewa su tsere a Kaduna

Yanzu-yanzu: Mazauna gidan gyaran hali sun yi yunkurin ballewa su tsere a Kaduna

Mazauna gidan gyaran hali a jihar Kaduna sun yi yunkurin balle gidan gyaran halin bayan rikici ya barke a kan barkewar cutar coronavirus a kasar nan, jaridar SaharaReporters ta ruwaito.

'Yan gidan gyaran halin, wadanda suka ji tsoron samun cutar sakamakon rashin isasshiyar iska mai tsafta da kuma kayan kariya daga cutar, sun taru da yawansu a safiyar yau Talata inda suka yi yunkurin ballewa su tsere daga gidan gyaran halin.

Jami'an tsaro da suka dinga harbi a farfajiyar gidan gyaran halin don tsorata 'yan gidan gyaran halin tare da saisata komai.

A halin yanzu mutum daya ne ake tsammanin ya rasa ransa sakamakon rikicin amma jami'ai masu yawa sun samu raunika inda aka gaggauta mika su asibiti don taimakon likitoci.

Wani jami'i a gidan, wanda yayi magana da bukatar a sakaya sunansa a ranar Talata, ya ce bangarori da yawa na gidan duk sun lalace sakamakon barnar mazauna gidan.

Yanzu-yanzu: Mazauna gidan gyaran hali sun yi yunkurin ballewa su tsere a Kaduna

Yanzu-yanzu: Mazauna gidan gyaran hali sun yi yunkurin ballewa su tsere a Kaduna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Jerin kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

"An yi yunkurin fashe gidan gyaran halin kuma rikici ya barke. Ma'aikata da yawa sun samu raunika amma jami'an tsaro na kokarin kwantar da tarzomar," jami'in yace.

Idan zamu tuna, sanannun 'yan Najeriya sunyi kira ga gwamnatin kasar nan da ta rage mazauna gidan gyaran halin ta hanyar sakin masu kananan laifuka don hana yaduwar coronavirus.

SaharaReporters ta gano cewa, tunda mazauna gidan gyaran halin suka samu labarin bullar cutar a Najeriya, sun dinga kokarin ballewa su gudu tunda gwamnati ta kasa daukar wani mataki.

"Mun jawo hankulan gwamnatin tarayya da na jiha a kan su dauka matakin gaggawa don rage mutanen da ke gidan gyaran halin. A saki masu kananan laifuka da kuma masu hukuncin kisa wadanda suka dau sama da shekaru 10 kuma suke da shekaru 60 zuwa sama na haihuwa," A cewar majiyar.

"Ministan al'amuran cikin gida ya samu sakon kuma ya yi kira ga gwamnatin amma har yanzu babu abinda aka yi a kai. Daga karshe dai zai yuwu su balle gidan yarin kuma 'yan ta'adda masu hatsari za su koma neman abin yi a tituna," wata majiya mai kusanci da hukumar gidan gyaran halin ta sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel