Akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya bar Juventus bayan kungiyar ta shiga matsalar kudi saboda Covid-19

Akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya bar Juventus bayan kungiyar ta shiga matsalar kudi saboda Covid-19

- Akwai yiwuwar Ronaldo zai bar kungiuyar kwallon kafa na Juventus idan suka kasa biyansa kudaden da ya ke bukata

- Kungiyar na kasar Italiya tana fuskantar matsalan kudi sakamakon bullar annobar coronavirus da ta addabi duniya

- A baya-bayan nan ne Ronaldo ya amince da rage albashinsa domin ya taimakawa kungiyar farfadowa daga matsalar rashin kudin da ta fada

Akwai yiwuwar kungiyar Juventus za ta sayar da Christiano Ronaldo sakamakon halin rashin kudi da ta fada bayan bullar annobar coronavirus a kasar.

A cewar kafar yadda labarai na italiya II Messagero, akwai yiwuwar kungiyar ba za ta iya biyan dan kwallon albashinsa da sauran allawus ba na £500,000 duk sati.

Matsalar karyewar tattalin arziki da ya samu wasu kasashen duniya sakamakon bullar annobar ta Coronavirus ya saka kungiyar ta rage wa 'yan wasa albashinsu a cikin 'yan kwanakin nan.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun kone ofishin Yan sanda a Katsina (Hotuna)

Kuma akwai alamun cewa ko da an fara buga wasannin kwallo a Italy, kungiyar ba za ta iya cigaba da biyan albashi masu tsada ga 'yan wasar ta ba.

A cikin 'yan kwanakin nan, Ronaldo ya amince ayi amfani da albashinsa na watanni hudu domin ceto kungiyar da manajan kungiyar Maurizio Sarri.

Rage kudin ya saka kungiyar ta samu rarar Fan miliyan 80 da suka baya albashi na watannin Maris, Afrili, Mayu da Yuni.

Kungiyoyi da dama a Turai suna fuskantar matsalar kudi tunda aka dakatar da buga wasanni sakamakon bullar kwayar cutar.

Lionel Messi da takwarorinsa na Barcelona suma an rage musu albashinsu da kashi 70 cikin 100.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel