Jerin kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

Jerin kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

Duk da cewa cibiyar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cutar coronavirus a matsayin annoba wacce babu inda aka tsira daga sharrinta, akwai wasu kasashen duniya kadan da har yanzu cutar bata bulla ba.

Bayan fara sanin cutar da aka yi a Wuhan a watan Disamba na shekarar da ta gabata, an tabbatar da ta kama mutane a kalla 788,000 a fadin duniya tare da halaka a kalla 38,000.

Amma kuma, akwai kasashe 16 da har yanzu babu cutar ko alamarta.

A Afrikac, kasashe irin su Lesotho, Sudan ta Kudu, Yemen, Sierra Leone, Burundi da Malawi da ke Yammacin Sahara, har yanzu babu wanda ya kamu da cutar.

Kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba

Kasashen duniya 16 da ba a samu bullar Coronavirus ba
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Fusatattun matasa sun kone ofishin Yan sanda a Katsina (Hotuna)

A nahiyar Asia, kasashe irinsu Turkmenistan, Tajikistan da Korea ta Arewa duk babu labarin bullar cutar.

Akwai wasu kasashen da ke tsibirin Pacific wadanda aka sani da wuraren shakatawa, har yanzu ba a samu bullar cutar ba saboda a kebance suke da kuma rashin ci gabansu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wadannan yankunan sun hada da Tonga, Samoa, Vanuatu, tsibirin Cook, Niue da Tuvalu.

Cutar coronavirus ta yadu a kasashe a kalla 178 da kuma yankuna da dama na fadin duniya.

A duk kasashen, a kalla mutane 166,700 ne da aka samu da cutar suka warke garas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel