Coronavirus: Mutane 849 suka mutum a rana daya a Spain

Coronavirus: Mutane 849 suka mutum a rana daya a Spain

A ranar Talata, Gwamnatin Spain ta sanar da mutuwar mutane 849 cikin sa'o'i 24 sakamakon cutar Coronavirus. A yanzu mutane 8,189 ne suka mutu a fadin kasar

Hakazalika, a kwana daya an tabbatar da sabbin mutane 9,222 sun kamu da cutar. Jimillan wadanda suka kamu da cutar a ksar yanzu 94,417.

A duniya yanzu yawan mutanen da suka mutu sakamakn cutar sun zarce 38,000 kuma wadanda suka kamu da cutar sun kusa 800,000.

Abin takaici, ma'aikatan kiwon lafiya masu jinyar mutane suna kamuwa da cutar. A ranar Litinin, Al Jazeera ta ruwaito cewa ma'aikatan kiwon lafiya 12,298 da aka tabbatar sun kamu da cutar yanzu.

Wani farfesa a jami'ar Qurtuba dake kasar Spain, Jose Hernandez, ya bayyana cewa: "Wannan shine labari mafi tsoratarwa."

"Ayyuka sun yi asibitocin yawa, adadin ma'aikatan kiwon lafiya ya yi kadan dubi ga yawan marasa lafiya."

KU KARANTA: Coronavirus: Mutane biyu da suka kamu a Kaduna na kusa da El-Rufa'i ne - Gwamnatin jihar

Coronavirus: Mutane 849 suka mutum a rana daya a Spain

Coronavirus: Mutane 849 suka mutum a rana daya a Spain
Source: UGC

A bangare guda, Farashin danyen mai na Brent ya sauko zuwa $22 a kan kudin kowane ganga. Farashin man bai taba yin araha irin haka ba a cikin shekaru kusan 12 da su ka wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa a farkon makon nan ne farashin gangar danyan man ya lula kasa haka. Fiye da fam Dala $2.8 ya ragu da farashin gangar man na Brent.

A jiya Litinin da kimanin karfe 5:00 na yamma, ana saida gangar danyen man a kan fam Dala $21.76. A karshen makon jiya an saida gangar danyen man a $22.10.

Reuters ta ce rabon da kudin mai ya sauko kasa haka tun cikin Watan Maris a 2002. A cikin watanni 216 da su ka shude, danyen mai bai taba rasa daraja haka ba.

Wannan karyewa da mai ya yi a cikin ‘yan kwanakin bayan nan ne ya jawo gwamnatin Najeriya ta rage burin abin da za ta samu daga mai a wannan shekara ta 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel