COVID-19: Yadda na yi gwargwamaya da mugunyar cutar har na warke - Osowobi

COVID-19: Yadda na yi gwargwamaya da mugunyar cutar har na warke - Osowobi

Sa'o'i kadan bayan an tabbatar da cewa bata dauke da cutar coronavirus kuma an sallame ta daga asibiti, Oluwaseun Ayodeji Osowobo a ranar Litinin ta bayyana yadda tayi gwagwarmaya da cutar coronavirus.

Ta bayyana cewa tayi nasara inda tace: "Ni ce na halaka coronavirus. Nayi gwagwarmaya da ita kuma nayi nasara. Coronavirus ba busharar mutuwa bace. Mutane na iya warkewa."

Osowobu ita ce babbar daraktar kungiyar taimakon kai da kai da ke yaki da fyade mai suna StandtoEndRape.

Ta ce a kalla tana shan kwayoyin magani 31 a kowacce rana. Takwas da safe, 13 da rana sai kuma 10 da dare.

Mai rajin kare hakkin dan Adam din ta bayyana yadda ta dinga aman kwayoyin amma sai dai ta dogara da ORS bayan ruwan jikinta yayi karanci.

COVID-19: Yadda nayi gwargwamaya da cutar tare da irin wahalar sa na sha - Asowobi
COVID-19: Yadda nayi gwargwamaya da cutar tare da irin wahalar sa na sha - Asowobi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Labari da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan dokar Covid-19

Ta ce ta kamu da cutar coronavirus ne yayin da take neman wani aiki wanda daga baya ta rasa.

Ta jinjinawa Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu a kan ziyarar da ya kawo mata yayin da take jinyar.

Osowobi, wacce ta gujewa tsangwamar jama'a, ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter.

Tana cikin mutane biyar din da aka sallama a ranar Litinin daga cibiyar killacewa ta jihar Legas bayan ta warke.

Halin da ta tsinci kanta a kan cutar coronavirus ya kasance wahala da buri.

Ta yi alkawarin sakin bidiyon abinda ta fuskanta.

Osowobi ta ce: "Na dandana rashin dadin rayuwa. Nayi kokarin jajircewa amma kuma inaso in karfafa masu cutar guiwa. Na dawo Najeriya daga Ingila amma sai ja fadi ciwo. A matsayina na mai hankali, na killace kaina. Kafin dawowata, akwai kwagilar miliyoyin da zan saka hannu, duk na rasa su."

Ta kara da cewa, "Dole ta sa na killace kai a kuma na sanar da jama'a cewa nayi mu'amala da masu cutar coronavirus. Ni da kawata muka dinga kira NCDC don a gwada mu. Bayan diban jininmu, babu wani labarin sakamakon. Wajen karfe 12 na dare sai ga motar asibiti a gidana. Da gaggawa na tashi na fara kuka. Mun isa cibiyar killacewar amma sai da na dauka sa'o'i biyu kafin a shigar dani."

Ta ce, "Daga baya kuwa ma'aikatan jinyan sun iso inda suka dinga daukata kamar wata annoba. Babu wata tambaya a kan yadda nake ji, sai dai tambayoyi a kan tafiyar da nayi. Bayan sa'o'i biyu aka kaini gadona. Bayan kwanaki biyu sai aka kara kawo wani daga nan aka ci gaba da kawo wasu."

Bayan kwanaki kadan na fara tsananin ciwon, bana son cin abinci ga kuma yunkurin amai da zawo mara tsayawa. A tunanin mutuwa zanyi don har na fara tunanin wanda zai gaji gidauniyar tallafina ta StandtoEndRape" Ta kara da cewa.

Osowobi tayi bayanin yadda ta dinga shan magani kamar ba za su kare ba. "Ruwa, Abinci, sabulu da komai kuwa bana son ganinsu. Amma dole ta sa na dinga shan ORS don jiki na babu ruwa. Na jajirce ne sannan na rayu," a cewarta.

Amma kuma, Osowobi wacce ita ce mutum ta uku a Najeriya da ta samu cutar, ta ce daga baya sai aka nemi kwayar cutar aka rasa a jikinta, kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana.

Ta kara da cewa: "Bayan kwanaki kalilan, likitoci sun sanar dani albishir cewa bana dauke da cutar. Tuni kuwa na sanar da 'yan uwa da abokan arziki. An dau jini na amma shiru sai da kara kwanaki biyu ina shan magani. Sauran majinyatan sun dinga sha'awata kuma suna fatan zama irina. Bayan kwanaki kalilan ne aka sallameni bayan sakamako na biyu ya bayyana cewa bana dauke da cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel