Coronavirus: Mutane biyu da suka kamu a Kaduna na kusa da El-Rufa'i ne - Gwamnatin jihar
Kwamishanan kiwon lafiyan jihar Kaduna, Dakta Amina Baloni, ta tabbatar da cewa lallai mutane biyun da suka kamu da cutar Coronavirus a Kaduna wadanda suka hadu da El-Rufa'i ne. The Nation ta ruwaito.
Mun kawo muku rahoton cewa cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC a ranar Litinin ya alanta cewa an samu karin mutane biyu da suka kamu da Coronavirus a Kaduna.
Hakazalika a ranar 28 ga Maris, gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ya zama mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus a jihar.
A jawabin da Balori ta saki ranar Talata a Kaduna, ta ce jami'an kiwon lafiyan jihar na bibiyan wadanda suka hadu da gwamnan domin takaita yaduwar.
Ta yi kira ga mazaunan jihar su bi umurnin gwamnati suyi zamansu a gida domin takaita yaduwar annobar.

Asali: Facebook
Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya.
Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19 a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“
“Dai-dai Karfe 9:o0 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“
Ga jerin jiha-jiha
Lagos- 81
FCT- 25
Ogun- 3
Enugu- 2
Ekiti- 1
Oyo- 8
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-2
Rivers-1
Benue- 1
Kaduna- 3
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng