Rundunar Sojin Najeriya sun hallaka babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah

Rundunar Sojin Najeriya sun hallaka babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah

Dakarun Sojin Operation Lafiya Dole sunn hallaka wani babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah, tare da yan’uwansa yaN ta’adda yayin musayar wuta da Sojojin a Gorgi, karamar hukumar Damboa, ta jihar Borno.

Wakilin Diraktan yada labaran hedkwatar tsaro, Birgediya Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan ranar Litinin.

A Jawabin ya ce an samu kwato makaman AK-47 biyu, harsasain AK47, Roka, harsasan baro jirgin sama 273, dss.

Yace: “Labarin leken asiri ya tabbatar mana da cewa wani babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah, na cikin yan ta’addan Boko Haram da aka kashe a Gorgi.”

“Ya samu raunuka a musayar wuta kafin yaransa suka tafi dashi. Amma daga baya ya mutu. Ko shakka babu mutuwarsa babban asara ne ga shugabancin Boko Haram.”

Rundunar Sojin Najeriya sun hallaka babban kwamandan Boko Haram, Abu Usamah
DHQ Abuja
Asali: Original

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum na farko da ya kamu da Coronavirus a Oyo ya samu sauki, an sallamesa

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa hare-haren jirgin sama na rundunar Operation Lafiya Dole, ta kai ya yi sanadin halakan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram 1000 a batakashin da akayi ranar Litinin, a garin Gorgi, jihar Borno.

Jawabin ya ce hukumar ta yi rashin Sojoji 29 yayinda 39 suka jikkata a artabun.

Karin bayani kan lamarin, diraktan yada labarin ma’aikatar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana cewa sabanin jawabin da yayi da farko cewa 47 aka kashe, rahoto daga filin daga ya nuna cewa basu kai haka ba, 29 kadai aka kashe.

Yace: “Bayan harin, an samu wadannan rahotannin: An kashe Sojojin Najeriya 29 a faggen fama, an jikkata 39 a faggen daga sakamakon tashim bam cikin motar da ke dauke da makaman da aka kaiwa Sojojin.”

“Hakan ya sabawa adadin da muka fada da farko cewa mutane 47 aka kashe kuma 15 sun jikkata. Hakan na faruwa a lokacin yaki saboda gudun kada masu yada labaran karya su fadi adadin da bashi bane.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel